Nasir S Gwangwazo" />

Rashin Tsaro Na Kara Ta’azzara A Garin Abuja

A cikin shekaru hudu da su ka gabata garin Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya, ya kasance cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. A wancan lokaci, a na danganta garin da cewa, shi ne kadai wajen da mutane su ke barci da idanuwansu guda biyu a cikin wannan kasa, amma masu garkuwa da mutane sun fara cin karensu babu babbaka a cikin wannan birni a yanzu.
A cikin makonnin da su ka gabata, babu wata rana da ba a samun rahoton gaskuwa ko fashi da makami ko kuma ayyukan ta’addanci a cikin garin Abuja. Alal misali; makonni biyun da su ka gabata, a ka bayar da rahoton cewa, wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum takwas a kauyen Pegi da ke gundumar Kuje ta birnin tarayya.
An bayyana cewa, ’yan bindigar sun saka kayan aikin sojoji, inda su ka bude wa wasu motoci guda biyu wuta, wadanda su ka hada da kirar Toyota da Nissan Frontier, inda su ka yi awon gaba da mutane da dama. Haka kuma kafin wannan a makon ma, wasu ‘yan bindiga wadanda a ke kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne su ka kashe wani mutum mai suna Ayuba tare da yin garkuwa da ’ya’yansa guda biyu a yankin Yebu da ke karamar hukumar yankin Kwali a cikin garin Abuja.
Hakazalika, a cikin watan da ta gabata, a ka yi garkuwa da wasu mazauna garin Abuja har mutum biyar tare da wasu daliban jami’an Baze Unibersity da ke garin Abuja, yayin da a ka saki wata daga cikin wadanda a ka sace mai suna Aishat Ardo bayan da mahaifinta ya biya kudin fansa ta Dala 15,000.
LEADERSHIP A YAU ta gano cewa, lamarin wasu mayaudaran direbobin tasi da ke yi wa fasinjoji fashi da a ke kira da suna “One Chance” ya na kara a ruwa a garin na Abuja, inda ta kai ga wasu fusatattun matasu su ka kashe wasu mutum uku da a ke zargi a yankin Dutse Alhaji cikin watan da ta gabata.
Wannan lamarin sata da motoci ya na kara ta’azzara a garin Abuja. Ya na da matukar mahimmanci a san da cewa, motoci kirar Toyota Sienna, Toyota Corolla S, Toyota Camry da kuma Mazda su ne barayin ke amfani da su kafin su juya zuwa motocin haya. Abin takaicin dai shi ne, ‘yan sanda sun tabbatar da cewa kullum sai sun samu wannan rahoton a wurare kamar wajen wanke mota da kasuwanni da wuraren ibada da wuraren bukukuwa da makarantu da kuma wuraren shakatawa.
Mazauna garin Abuja su na fama da wannan mummunan labari, musamman a kwaryar garin da wasu kananan hukumomin garin, inda su ka bukaci gwamnati da jami’an tsaro da su kawo karshen lamarin.
Masu aikatana wannan mummunan aika-aika su na cin karensu babu babbaka ne sakamakon rashin hasken wutar lantarki a wasu wurare da ke cikin garin Abuja.
A matsayinsa na birnin tarayyar Nijeriya, a ganinmu bai kamata garin Abuja ya fuskanci matsalar rashin tsaro ba. Abinda a ka fi sanin birnin da shi shi ne, cin hanci da rashawa a ofisoshin gwamnati da dabarun kawar da tunani ta hanyar tafka magudi, amma ba matsala irin wannan ba.
Garkuwa da mutane da yin fashi a motoci da fashi da makami duka dai ya saba da zamantakewar al’umma, sakamakon yunwa da fatara da kuma matsanancin rayuwa da al’umma su ke ciki ne ya haifar da wannan matsaloli.
Ra’ayinmu dai shi ne, yakamata gwamnati ta kashe Dala miliyan 470 domin magance matsalar tsaro. Mu na kira da a sake karfafa na’urar talabijin a garin Abuja wanda wata kamfanin kasar China da kamfanin ZTE Nigeria Limited ta samar a shekarar 2010, domin su samar wa ‘yan sanda bidiyo da bayanai na tsaro. Wannan zai kara dakile matsalar tsaro ta hanyar fasahar zamani. Wannan aiki na kafa na’urar bidiyo baya aiki ko sannan ba a samar da shi a ko’ina da ke fadin garin Abuja ba. Haka kuma mu na bai wa jami’an tsaro shawara da su tsananta tsaro a cikin garin Abuja domin kawo karshen wannan lamari. Mu na kira da a samar da jami’an tsaro ta musammann da zai yi yaki da masu garkuwa da mutane da kuma sauran ayyukan ta’addanci da a ke yi a wannan gari na Abuja.
Bugu da kari kuma, mu na kira ga hukumar da ke kula da babbar birnin tarayya da su gyara wutar lantarki da ke kan hanyoyi a kan manyen tituna da ke fadin garin Abuja. Haka kuma, ya na da kyau a samar da na’urar daukar bayanai a dukkan manyen tituna da ke Abuja, mun tabbatar da cewa zai rage matsalolin tsaro a garin Abuja. Bai kamata a ce babbar birnan tarayyan Nijeriya ta na fuskantar matsalokin tsaro ba, musamman wannan lokaci da kasar ke bukatar masu zuba hannun jari. Ya kamata garin Abuja ta kasance ita ce gari mafi tsaro, domin kiran masu zuba hannun jari.

Exit mobile version