Rashin Tsaro: Shugaban Rundunar Soji, Irabor, Ya Gana Da Tsoffin Janarori Daga Kudu-maso-yamma

Daga Sulaiman Ibrahim

 

Babban hafsan hafsoshin tsaro (CDS), Janar Lucky Irabor, ya gana da manyan hafsoshin soja daga Kudu maso Yamma da suka yi ritaya don tattauna hanyoyin fita daga kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a yanzu.

Da yake magana a lokacin bude taron a ranar Alhamis a Hedikwatar runduna ta 2 ta sojojin Nijeriya, Ibadan, Irabor ya ce wannan wani bangare ne na kokarin da ake yi da nufin gano musabbabin matsalolin tsaro a kasar nan.


Ya ce an gudanar da taron ne domin samun ilimin mafita daga halin da Nijeriya ke ciki daga kwararru na jami’an da suka yi ritaya da sauran masu ruwa da tsaki.

“Duk wata kwarewa da mafita da aka samu daga taron za su taimaka wajen magance kalubale iri-iri na tsaro a Nijeriya.

“Tare da dumbin kwarewar ku da ilimin da kuka samu tsawon shekaru, mun yi imanin babu wata kyakkyawar hanyar fice wa daga halin da Nijeriya ke ciki wacce ta fi taku kwarewar.

“Kun fi cancanta da ilimi a kan al’amuran tsaro kuma saboda wannan, muka gayyato ku nan. Kun san sha’anin tsaro a yankinku, ”in ji Irabor.

Exit mobile version