Rashin Tsaro: ‘Yan Nijeriya Dubu 40 Ne Suka Yi Hijira Zuwa Nijar- Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar dinkin duniya ta ce matsalolin tsaro a arewa maso yammacin Nijeriya, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga sun tilastawa sama da mutum dubu 40 tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar cikin watanni 10 da suka gabata.

Rahoton majalisar dinkin duniyar ya ce a ranar 11 ga watan Satumba kadai, ’yan gudun hijira akalla dubu 2 da 500 ne suka tsere zuwa Nijar, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

Yayin ganawa da manema labarai, mai jami’in da wakilci majalisar dinkin duniyar wajen wallafa rahoton, Babar Baloch, ya ce Katsina, Zamfara, da Sakkwato sune jihohin da matsalar tsaron ta fi kamari cikin watanni 10 da suka gabata.

A makon jiya gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da wani rahoton majalisar dinkin duniya kan matsalolin tsaro a kasar.

Cikin wata sanarwa, kakakin shugaban Nijeriya Malam Garba Shehu, ya ce rahoton na wakiliyar majalisar dinkin duniya Agnes Callarmard, bai yi adalci ba, wajen fayyace gaskiyar halin da ake ciki kan tsaro a Najeriya ba.

Cikin rahoton, majalisar dinkin duniyar, ta bayyana Najeriya a matsayin kasar dake fama da rikicin cikin gida a sassanta da dama, wadanda ke dada kamari, ko da yake rahoton ya yabawa gwamnati kan nasarorin da ta samu kan Boko Haram.

A bangaren tashe-tashen hankula a sauran sassan kasar, rahoton majalisar dinkin duniyar ya bayyana rashin bibiya, talauci, sauyin yanayi da kuma yaduwar muggan makamai a tsakanin jama’a a matsayin wasu daga cikin matsalolin da ke rura wutar matsalolin tsaro da rikice-rikicen da Najeriya ke fuskanta.

Sauran matsalolin a cewar majalisar dinkin duniya sun hada da, yadda gwamnati ke yin amfani da karfi wajen dankwafe wasu kungiyoyi a Najeriyar da suka hada da ‘yan shi’a, ‘yan Kungiyar IPOB da aka haramta, da kuma al’ummar Ogoni.

Exit mobile version