Sulaiman Ibrahim" />

Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Sake Barkewa A Katsina

Mazauna kauyakun Katsina cikin fushi da safiyar yau sun toshe hanyar Kankara-Katsina suna cike da yin zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu game da hare-hare a garuruwansu da ‘yan bindiga ke kaiwa

Mazauna garuruwan sun yi amfani da dogayen bishiyoyi don toshe hanyar da ke kusa da kauyen Marken Dogon Ruwa da ke karamar hukumar Dutsinma, suna mai da masu motoci baya.

A yanzu haka daruruwan motocin haya da na masu zaman kansu suna nan tsaye a kan hanyar.

‘Yan bindiga sun afka garuruwan Sanawa, Bera, Turare da Dogon Ruwa dake Makera a karamar hukumar Dutsinma a daren jiya Laraba.

Wakilin mu ya samu labarin cewa tuni rundunar ‘yan sanda ta isa wurin, suna kokarin kwantar da hankulan mutanen garin don sake bude hanyar.

Wannan ita ce zanga-zanga ta biyar da mazauna garin Katsina suka nuna game da hauhawar rashin tsaro a jihar cikin watanni biyu da suka gabata.

An gudanar da zanga-zangar ne a garuruwa daban-daban, kamar Daddara da ke cikin karamar hukumar Jibia, Yantumaki dake karamar hukumar Danmusa da ‘Yankara dake cikin karamar hukumar Faskari.

Exit mobile version