Connect with us

RIGAR 'YANCI

Rashin Wakilci Nagari Ne Matsalar Gundumar Ward D – Hon. Babi

Published

on

A daidai lokocin da hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kogi (SIEC) ke shiryen-shiryen gudanar da zabukan kananan 21 da ke fadin jihar a ranar 5 ga Satumbar, 2020, dan takarar kansila mai neman wakiltan mazabar gundumar ‘Ward D’ da ke karamar hukumar Lokoja a karkashin jam’iyyar APC, Hon. Muhammed Gambo Babi, ya ce, babbar matsalar da ke addabar gundumar ita ce rashin wakilci nagari da kuma kyakkyawan shugabanci wadanda gundumar ta rasa tun tale-tale.

Hon. Babi ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke zantawa da wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU a jiya Lahadi.
Ya ce, “na tsaya takarar neman kansila ne domin ceto mazabar gundumar ‘Ward D’ daga rashin wakilci na gari da gundumar ke fama da shi shakaru da dama, kuma na dauki alkawarin samar da kyakkyawan wakilci ga al’ummar gundumar ta ‘Ward D’ wadanda suka dade basu sha romon dimukradiyya ba” cewar Hon Babi. Dan takarar ya kuma yi alkawarin cewa idan har al’ummar mazabarsa suka bashi daman ya wakilce su, da yardan Allah ba zai basu kunya ba,inda har ma kara da cewa manyan kalubalen da jama’ar gundumar ta ‘Ward D’ su ke fuskanta a yanzu sun hada da rashin ruwan sha da hanyoyi masu inganci musamman hanyar data ratsa unguwar kura wanda a yanzu bata da kyaun gani, sannan yayi alkawarin gabatar da kudurin janyo hankalin gwamnatin karamar hukumar Lokoja na ganin ta gyara hanyar wanda ke ciwa jama’ar yankin unguwar tuwo a kwarya.
Hon Babi ya kuma ce zai gabatar da kudurori dabam dabam a zauren majalisar dokokin na karamar hukumar ta Lokoja da zasu inganta rayuwar jama’ar mazabarsa ta gundumar Ward “D”. Har ila yau yayi kira ga sauran yan takarar karkashin jam’iyyar APC dasu janye masa tare da bashi hadin kai don ci gaban jam’iyyar da kuma gundumar ta ‘Ward D’ gaba daya.
Daga nan ya yabawa gwamna Yahaya Bello a bisa kudurinsa na samar da romon dimukradiyya ga daukacin jama’ar jihar Kogi.
Ya kuma jinjinawa gwamnan a kokarinsa na samar da kwararan matakan tsaro da kuma kare lafiya da dukiyoyin jama’ar jihar Kogi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: