Rashin Wutar Lantarki Na Dakushe Kasuwanci A Maiduguri

Gwamnatin Masar

Daga Maigari Abdulrahman

Kwanan baya, Boko Haram sun sake lalata ma’adinin kayan lantarki Jihar Borno da ke kusa da Maiduguri, babban birnin Jihar. Hakan ya haifar da illa da cikas ga mazauna jihar, shawo kan matsalar kuma dai ya ci tura.

Kimamin watanni hudu kenan ba wutar lantarki a Maiduguri tun bayan ta’asar Boko Haram din a kan ma’adinan lantarkin. Rashin wutar ya haifar da tabarbarewar kasuwanci, karuwar matsalar tsaro, da takura a cikin jama’a.

Saboda tsarin garin, Maiduguri ta kasance cibiyar kasuwanci. Ta hada iyakoki da kasar Chadi, Kamaru, da Nijar. Wanda ta Najeriya su ke shigo da kayan masarufi, Maiduguri ce hanyar shige da ficen nasu.

Wani mai dunkin keke, Bana Bukar mai shekaru 35, ya koka kan yadda rashin wutar ya haifar da tabarbarewar kasuwanci, rahsin wutar ya sa ba zai iya yin aikin dunkin salla kamar yadda ya dace ba, in ji shi.

“Muna da mashuban kayan aiki fiye da 12 amman iya biyar ne kadai mu ke iya anfani da su. Hakika matsalar wuta na dagula mu kuma tana taba kasuwanci,” in ji shi.

A jami’ar Maiduguri, haka lamarin yake. dalibai da dama ne zaune a gaban shago su na cajin wayoyi hannun su, kamar yadda wakilinmu ya gani. Haka su ke faman neman cajin abubuwan wuta a shagunan yan kasuwa da ke makarantar.

Wani mai shago da dalibai ke caji a shagonsa,ya bayyana cewar, “Rashin wutar ya kawo mana cikas ba kadan ba. Abubuwa sun yi tsanani, kan haka nake tausayin daliban na kuma yanke shawarar taimakonsu. Idan ka zo da yamma, za ka tarar cike da dalibai.”

“Ina sayen man inji na 8,000 a rana. Akwai rana kuma ga azumi, saboda haka mutane kan so abin sanyi yayin buda baki. Gaskiya akwai wahala matuka, ya kamata gwamnati ta dauki dukkan matakin da ya dace don ganin ta gyara wutar,” cewar Malam Abdullahi Mai Shago.

Akwai rahotannin da ke cewa ma, wasu kananan yan kasuwa na rasa kasuwancinsu sakamakon matsalar da rashin wutar ya haifar.

Rahsin wutar ya shafi kowane bangare na al’umma, matasa, matan aure, ‘yan kasuwa da sauran su, hakan ya zama dalilin karuwar ayukkan barna.

Ba Jidda Ayayi, wani mai fashin bakin al’amurra, ya ce rahsin wutar ya haifar da karin talauci a cikin al’umma.

“Rashin wutar, babu ko tantama, ya haifar da tashin farashin kayayyaki, da kuma tsanani. Ga kuma rana da ake fama da ita. Kodayake dai wannan zai habbaka samun kudin masu gyaran inji, to amman mafiyayawan al’umma sun takura,” in ji shi.

“Rahsin wutar ya tilasta magidanta sayen fetur domin sa wa inji wanda hakan karin kashe kudi ne, ba tare da sun samu karin wasu kudin ba. Haka suma ‘yan kasuwa,”in ji shi.

Shugaban wata kungiya kan masarautar Borno, Hassan Boguma, ya ce, duk da dai Sojoji na kokari a yaki da Boko Haram a Jihar, to amman akwai bukatar su sake karatun ta natsu da fiddo da salon dabarun yaki. A cewar sa, sojojin na da matsalar dabarun yaki.

Shugaban, wanda ya koka kan illar da rahsin wutar ya haifar, ya yi kira ga gwamnati da kanfanin wutar lantarki na kasa da su yi iya bakin kokarinsu na ganin an gyara wutar.

Exit mobile version