Connect with us

RAHOTANNI

Rasuwar Ajimobi: Bilya Asasco Ya Yi Ta’aziyya Ga Ganduje

Published

on

Shugaban kungiyar ci gaban al’umma ta ‘CPC’ na karamar Hukumar Ungogo, Alhaji Bilya Asasco ya bayyana rasuwar tsohon Gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi da cewa babban rashi ne, ba ga al’ummar jiharsa kadai ba, har ma da kasa baki daya, inda mika ta’aziyyarsa ga Gwamnan jihar Kano, Dk. Abdullahi Umar Ganduje.

 

Ya ce tsohon Gwamnan anini ne na hakika kuma suruki ne ga al’ummar jihar Kano, don haka wannan babban rashi ne gare su, don haka yana mika sakon ta’aziyyarsa ga Gwamna Ganduje da iyalinsa bisa wannan babban rashi, da fatan Allah ya yi masa gafara.

 

Da ya juya kan cika shekaru biyar na Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje akan mulki kuwa, ya ce ya samar da gagarumar nasara ga ci gaban jihar Kano, cikin wadannan shekaru.

 

Ya ce, Gwamna Ganduje ya yi abin da ba a yi a gwamnatocin da suka gabata, ya kafa tarihi a kasar nan da Gwamnonin Nijeriya suka gamsu suka yarda shi ne Gwamna da ya fi kowanne kokari da rike talakawansa da ciyar da su gaba.

 

Alhaji Bilya Asasco Bachirawa ya ci gaba da cewa, fatansu ga Gwamna Ganduje shi ne Allah ya ba shi damar ci gaba da sauke nauyi na al’umma da ya dora masa, ta ci gaba da hakuri da juriya da yake yi, wanda suke da yakinin zai ci gaba da samun nasara sakamakon hakurinsa.

 

Daga nan ya yi nuni da cewa, Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje yana gudanar da ayyuka tsakani da Allah, wanda ake ganinsu da idanu ake tabawa ake takawa a dukkan sassa na fadin jahar Kano.

 

Ya ce Gwamna Ganduje a wannan hali da ake ciki na annoba ya tashi ka’in-da-na’in wajen ganin an kauda cutar a jahar Kano ta daukar matakan kariya daban-daban da kuma yin addu’o’i da ake yi na neman kariyar Ubangiji daga wannan annoba da sauran masifu da ake fama da su a kasar nan baki daya. Wannan ta sa ake samun sauki na yaduwar Korona, kullun sauka take.

 

Alhaji Bilya Asasco ya ce a yankinsu na karamar Hukumar Ungogo an gina musu Makarantu da asibitoci, ga hanyoyi na burji, an yi tituna mai kwalta, baya ga Ofishin ‘yan sanda da aka yi suna yi wa Gwamna Ganduje godiya akan wannan kulawa da yake ba su.

 

Shugaban na CPC reshen karamar Hukumar Ungogo, Alhaji Bilya Asasco ya nuna jin dadinsa da godiya ga shugaban Hukumar Ilimin bai-daya ta jahar Kano, Dokta danlami Hayyo bisa yadda yake kulawa da ci gaban bunkasa ilimi tun daga tushe, wanda hakan ya taimaka sosai wajen bunkasa ci gaban ilimi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: