Connect with us

LABARAI

Rasuwar Falakin Katagum Babban Rashi Ne Ga Jihar Bauchi, Inji Umar Sade

Published

on

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Bauchi, Alhaji Umar Ibrahim Sade ya bayyana cewa Gwamnati da al’ummar Jihar Bauchi sun yi babban rashi na rasuwar Kwamishinan ma’aikatar raya yankunan karkara na jihar Bauchi Injiniya Mahmood Abdullahi Abubakar Falakin Katagum, wanda ya rasu a kwanan nan.

Kwamishinan ya bayyana alhinin sa ne cikin sakon ta’aziyya da ya aikewa manema labarai a Bauchi, ya ce “Duk mai rai mamaci ne, kowa kuma da lokacinsa. Mun yi rashin bawan Allah, mai yawan tuna Allah da yawan ambatonsa, mutum mai basira, mu a majalisar jihar Bauchi mun yi rashin abokin aiki haziki, jajirtacce mai tunani da hangen nesa ga kuma kaifin hankali, ba za mu mance da irin gudummawar da yake bayarwa ba wajen gina jihar nan da al’ummarta ba,” A cewar shi

Kwamishinan ya kara da cewa, Falakin Katagum mutum ne mai kaunar jama’arsa, mutum ne wanda in abu yayi nauyi shi dai a kullum yana tare da mafi yawan abin da al’ummarsa suke so.

Kwamishinan ya roki Allah ya ji kansa ya gafarta masa ya kuma isar da ta’aziyyarsa wa Gwamnan jihar Bauchi, da Mai martaba Sarkin Katagum da daukacin jama’ar jihar baki daya.

Wakilinmu ya labarto cewar an haifi marigayi Injiniya Mohammed Mahmood Abdullahi Abubakar ranan 16 ga watan Maris 1965 a garin Azare, da ke jihar Bauchi, ya yi makarantar Firamare a Gyallesu  da ke Zariya daga 1971-1977, ya halarci kwalejin Al-Huda-Huda da ke Zariya 1977 -1982, ya kuma halarci Kwalejin kimiyya da koyon sana’o’i da ke Kaduna inda ya karanta ilimin zanen taswirar gine-gine  ya kuma yi Diploma kan harkar Injiniya dukka a 1988, Ya kuma samu takardar shaidar babbar Diploma kan aikin Injiniya a 1992, ya kuma yi karatun digiri na biyu a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi a 2013 ya na cikin kungiyar Injiniyoyi na kasa.
Advertisement

labarai