Rasuwar Sarkin Hausawan Kasar Ebira Ya Girgiza Ni –Hon Abdulrazak

Daga Ahmed Muhammed Danasabe,

Shugaban qaramar hukumar Okene dake Jihar Kogi, Honarabul Abdulrazak Muhammed ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar daya daga cikin sarakunan yankin kuma Sarkin Hausawan qasar Ebira, Alhaji Baba Sale, wanda Allah yayi wa rasuwa a ranan Litinin 18 ga watan Oktoban 2021.

Shugaban qaramar hukumar, a saqonsa ta ta’aziyya ya bayyana rasuwar basaraken gargajiyan kuma shugaban al’umma a matsayin abin takaici kuma mai ciwo, yana mai qari da cewa rashinsa zai haifar da wagegen gibi da zai yi wuyar cikewa a qasar ta Ebira, idan aka yi la’akari da dimbin gudunmawar da marigayin ke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin,inda har ma

Hon Abdulrazak ya tuno gagarumin gudunmawar da marigayi Sarkin Hausawan a matsayinsa na daya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki yake bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin fulani makiyaya da manoma yan asalin yankin na qasar Ebira.

” Al’ummar Okene za suyi kyewarsa saboda gaskiyarsa da adalcinsa kuma iya gudanar da kyakkyawan shugabanci” Inji Shi.

Shugaban qaramar hukumar daga nan yayi addu’ar Allah ya jiqan marigayi Alhaji Baba Sale da rahama da kuma baiwa iyalansa da jama’arsa haqurin jure rashinsa.

Exit mobile version