Connect with us

RIGAR 'YANCI

Rasuwar Sarkin Numan: Adamawa Ta Bada Kwanaki Uku Na Zaman Makoki

Published

on

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da fara zaman makokin kwanaki uku a matsayin karramawa da juyayin mutuwar Mai Martaba Sarkin Numan kuma Hama Bachama, Marigayi Honest Irmiya Stephen.

Cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in yada labaran gwamnan Humwashi Wonoaikou, ta ce a hukumance gwamnati ta ayyana zaman makokin kwanaki 3, domin juyayin rasuwar sarki Irmiya Stephen, (Kwire Mana Kwafrato II).
Haka kuma sanarwar ta bada umurni ayi kasa-kasa da tuta, da zai fara daga yau litinin a lokutan aiki, zuwa ranar Laraba, domin juyayin marigayin da ya mutu ranar Lahadi.
Ta ce “lokutan zaman juyayin ya fara ne daga yau litinin 29/6/2020 a fadin jihar Adamawa”.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: