Daga Bala Kukkuru,
Sarkin al’ummar Hausawan Ikate Malam Mustafa Musti, kuma shugaban kasuwar sayar da dabbobi dake Karamar Hukumar Aja ta cikin birnin lkko, ya bayyana cewar, rasuwar shuwagabanni al’ummar Arewacin Nijeriya mazauna Legas guda uku a cikin shekara daya kacal ta girgiza ‘yan Arewa A Legas.
Sarkin na al’ummar Arewacin Nijeriya mazauna unguwar Ikate dake cikin garin Legas ya yi wannan tsokaci ne a unguwar Aja a lokacin da yake karbar gaisuwa tare da rasuwar marigayi shugaban Barebari na Jihar Legas Alhaji Mustafa Mohammed, wanda Allah ya yi masa rasuwa a sanadiyyar hadarin mota a Meduguri a kan hanyarsa ta zuwa Karamar Hukumar Mafa dake Jihar Barno da fatan Allah ya jikansa da rahama.
Ya cigaba da cewa marigayi sarkin Barebarin mutun wanda ya san ya kamata mai kishin addinin Musulunci da son cigaban al’ummarsa, ya yi gwagwarmaya kwarai da gaske a lokacin rayuwarsa a wajen kare hakkoki tare da mutuncin al ummar Arewacin Nijeriya mazauna Legas, da fatan fatan Allah ya jikansa, ya kara da cewa al’ummar Arewacin Nijeriya mazauna legas sun samu jarabta kwarai da gaske a wajan rasa gwar zayen shugabannin su a Legas.
Sannan kuma ya ba da gudum mawar sa awajan hada kawunan al umma tareda kawo zaman lafiya a Legas da kewayanta baki daya in ji shi da fatan Allah ya kawo masu wadansu shugabannin da za su maye gurbin wadancan shuwagabannin da suka rigamu gidan gaskiya wajan aikata ayyukan alheri.
Sannan kuma ya cigaba da shawartar sarakunan Hausawa mazauna cikin garin Legas da sauran shugabanni da su cigaba da hada kawunan junansu domin samun cigaba da zaman lafiya.
A karshe sarkin na Ikate ya ce yana Isar da sakon godiyarsa ga al ummar Jihar Legas in ji shi musam man kwastomomin shi masu zuwa kasuwar shi domin sayan dabbobi yana yima kowa fatan alheri ya ce kuma ya tanadar masu da manya manyan dabbobi domin biyan bukatun kansu da fatan Allah ya cigaba da zaunar da al’ummar Nijeriya lafiya.