Rawar Da Hakuri Yake Takawa Tsakanin Ma’aurata

Hakuri

Tare da Hafsan Moh’d Arabi,

Assalamu Alaikum! Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan shiri mai suna Uwargida Sarautar Mata…

Tofah Uwargida da ke nake! Shin ko kin san hakuri yana taka rawar gani a tsakanin Ma’aurata? Idan ba ki sani ba ki gyara zamanki yau ‘Topic’ dinmu a kan HAKURI zai tattauna in sha Allahu.

Tabbas! ana samun Mata wadanda sam ba su da hakuri ku san hanyar ma da ya biyo ba su san shi ba. Inda za ka ga mace ta zake tana fadin aibukan mijinta kan ta fadi alkairinsa sai ta fadi sharrinsa sau dari. Haka kuma ko abu ne ya gifta tsakaninsu ba ta iya dannewa har gaban yara ko kuma ta zauna ta dinga fadin laifukan mijinta da fada musu abubuwan da bai kamata ace tana fada ma ‘ya’yansu ba. Yana da kyau ki sani ‘yar uwa kina bata tarbiyar ‘ya’yanki da kuma saka musu kiyayyar mahaifinsu inda komai ya fada musu da gyara ba za su dauka ba kuma ba za su taba ganin shi da mutunci ba sai dai ya zamana a kullum azzalumi mugu a idanunsu wanda ba kowa yake zalunta ba irin uwarsu. Haka za su taso suma su daura ‘ya’yensu a kan wannan turbar. Shi yasa ake cewa inka baiwa ‘ya mace ilmi al’umma ka koyar. Shin ke irin ilmin da zaki koyar da ‘ya’yanki kenan? Yana da kyau mu koya hakuri gurin danne matsalolinmu da hakuri.

Labarin Uwargida da Amarya…

Akwai wasu Mata Amarya da Uwargida sai ya kasance duk inda ka zaga ba abin da za ka ji na alkairi kan wannan Amarya sai dai ka ji alhairai da yadda jama’a ke tausaya ma Uwargidan. Hakan kuwa ya faru ne sanadiyyar karkatar da hankalin Maigidan zuwa ga Amaryar wanda mutane ke ganin cewa asiri ita waccan Amaryar ta yi. Maigidan ya kasance me adalci tsakanin Matayen nasa sai dai ba zaka taba jin adalcinsa gun uwargidan nasa ba sai gun Amaryar nan. Haka Rayuwar gidan ta kasance makusantan Mijin da abokai sukan yi mamakin yadda yake yaba hakurin wannan Amaryar nasa musamman a irin dabi’unsa na saurin fushi da fada, hakan baya sa wa Amaryar nan ta sauya mishi fuska ko yaga canji duk inda ya zauna ya kan fada ya yabe ta sabanin Uwargidansa wanda ko maganarta ba ya so. Uwargidan ba hanya da yadda za ta hada su kota rabasu bata biba sai dai duk abin da ta yi kanta yake komowa ga rashin hakuri kome ya mata saita baza duk kankantarsa. Ku san bata fahimci illar da take ma kanta ba saida ta rasa kan mijin nata gaba daya kafin cikin ikon Allah yau da gobe Allah ya taimake ta ta hada kai da Amaryarta ta gyara wasu daga dabi’unta.

DARASI:

  1. Shin sunan Mijinta data bata kan mara Adalci zai taba goge wa gun mutane koda ita da Mijinta suna zaman lafiya ta shiryu? A’a shi ne amsar dan ko abu ne da ba zai taba goguwa ba wanda bashi kadai ta zubarwa mutunci idon duniya ba hatta kanta da ‘ya’yanta, don kuwa ba za su manta da koyarwarta ba.
  2. Abokiyar zamanta da ta bata shawara kuna ganin mutane za su daina mata wani kallo? Tabbas! A’a dan mutane basu mantawa koda wanda ya yi abun ya manta. Ta koya ma ‘ya’yanta kin abokiyar zamanta wanda lallai hakan zai shafi ‘ya’yansu su ta so cin kiyayyar juna. Wanda hakan na nuna ta ruguza hadin kan gidanta da hannunta Allah ya sa mu dace.

Ba wai ba maza hakan ba ne masu hali na rashin hakuri a nan nake jan hankalinmu baki daya Maza da Mata da mu yi koyi da ma’aikin Allah (S.A.W).  Wajen hakuri da abokan zamanmu don ba ‘ya’yayenmu tarbiya ta gari. Allah ubangiji yasa mu dace ameen Ina fatan za mu gyara, sai Allah ya hadamu a wani filin insha Allahu.

Exit mobile version