A kallan Dala miliyan dari uku da saba’in ne ake sa ran Bankin Duniya zai kashe wajen ayyukan raya kasa a jihar Neja.
kwararre a shirin raya kasa, Farfesa Odilili Ojukwu ne ya bayyana hakan a taron kwararru kan canjin yanayi mai taken ACRESAL da hukumar NEWMAP ta shirya dan jin shawarwarin masana daga bangarorin ma’aikatun gwamnatin jiha, da ya shafi ma’aikatar filaye da gidaje, ruwa, da ma’aikatar kula da jin dadin mata, sadarwa da kananan hukumomi.
Taron wanda aka shirya shi da jin shawarwari da bayanai ta yadda shirin Bankin Duniya zai yi daidai da sauyin yanayi ta yadda za a bunkasa bangaren noma da samar da ayyuka ga jama’a dan rage radadin talauci.
Shirin wanda zai mayar da hankali akan irin gudunmawar da ma’aikatun gwamnati zasu bayar da yadda wadanda yankunan su shirin ya shafa zasu anfani shirin.
Shirin mai taken Agro-climatic resilience in semi-arid landscapes, kamar yadda kodinetan hukamar NEWMAP, Alhaji Usman Garba Ibeto ya ce wannan shirin ya janyo kwararru ta yadda zasu taimaka wajen samun nasarar aikin kamar yadda bankin duniya ta bukata, wanda wajibi ne a hada kai da jami’an gwamnati dan samun shawarwari ta yadda al’ummar da abin ya shafa zasu anfana bayan gudanar da ayyukan raya kasa da samar da gurabun ayyukan ga jama’a duba da irin halin matsi da rashin aikin yi ya yiwa mutane katutu.
“Daga cikin kukurin mu bayan gabatar da ayyukan raya kasa ga jama’a, muna kokarin gabatar da ayyukan yi ta hanyar bada tallafi ga jama’ar da abin ya shafa, musamman wajen horar da su sana’o’in hannu dan samun madogarar rayuwa, ” ya ce.
Ya kara da cewa, Wadannan kwararrun da suka kware a bangarori daban daban za su taimaka mana da shawarwarin da suka dace wajen samar da ruwan sha mai tsafta, tallafawa mata, inganta aikin noma, da samar da yanayi mai kyau duba da irin kalubalen da canjin yanayi ya haifar.”
Hon. Andrew Jagaba, shi ne shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dokokin jiha, yace majalisa za ta tabbatar ta samar da ingantattun dokokin da za ta baiwa gwamnatin jiha kwarin guiwar bada gudunmawa ga shirin NEWMAP, domin Neja na bukatar ayyukan wannan hukumar saboda kalubalen ambaliyan ruwa da zaizayar kasa da wasu sassan jihar ke fuskanta.
Na ziyarci wasu sassan da hukumar ke gudanar da ayyukanta a halin yanzu wanda na shaidawa shugaban majalisar dokokin jiha, Rt. Hon. Abdullahi Bawa Wuse irin cigaban da ake samu, saboda haka mu a majalisa a shirye mu ke wajen baiwa wannan shirin goyon baya ta yadda jihar nan za ta anfani shirin tallafin bankin duniya na inganta rayuwar al’umma ta yadda za a iya fuskantar kalubalen canyin yanayin da duniya ke fuskanta.