Sulaiman Bala Idris" />

Rayuka Sun Salwanta A Rikicin Da Ya Barke A Kaduna

Za Mu Dauki Tsattsauran Mataki –el-Rufa’

Daga Sulaiman Bala Idris

Akalla mutane tara ne suka rasa ransu jiya a wani sabon rikcin addini da ya barke a Kasuwar Magani, garin dake karkashin Karamar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Garin Kasuwar Magani yana da matsuguni ne a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia. Daga garin zuwa cikin garin Kaduna tafiyar Kilomita 36 ne.

A wata sanarwa wanda kakakin Gwamnatin Jihar Kaduna ya fitar, Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnatin Malam Nasiru el-rufai ta sha alwashin daukar tsattsauran mataki akan duk wanda aka kama da hannu a barkewar wannan rikici.

Wakilinmu ya bankado cewa sama da mutum 20 ne suka samu munanan raunuka a yayin da aka samu ata arangama tsakanin Matasan Musulmi da Kirista, wanda ake zargin ya samo asali ne daga tsabar rashin hakuri da juna da kai hankali nesa.

A sabon rikicin an samu salwantar dukiya mai dimbin yawa, wanda a kiyasi ana batun asarar miliyoyi ne, banda ababen hawa da wadannan matasa suka cinnawa wuta.

Ya zuwa tattara wannan rahoton ba a samu takamaimen musabbabin wannan rikici ba, amma majiyarmu ta bayyana wa LEADERSHIP A Yau cewa, rikicin na da nasaba ne da sauya addinin da wasu ‘yan mata biyu suka yi daga addinin Kirista zuwa Musulunci.

Wasu daga cikin al’ummar wannan yanki na Kasuwar Magani, Ahmadu Dogo da Jummai sun sanar da wakilinmu cewa, a yunkurin matasan Kiristoci da na Musulmin na ganin sun dakatar da ‘yan matansu daga yin mu’amalar soyayya da ‘yan daya daga cikin bangaren addini tare da komawa addinin ne musabbabin wannan rikici.Sannan kuma sun shaida mana cewa, mutum tara ne suka rasa ransu sakamakon wannan hatsaniya.

Sai dai Kantoman Karamar Hukumar ta Kajuru, Aminu Rabiu ya bayyana cewa, “Sabani ne tsakanin matasan Kirista da Musulmi ya haifar da wannan asarar rayuka, da dukiya mai tarin yawa.”

Sai dai Kantoman ya ce, tuni an dakile ci gaba da yaduwar rikicin sakamakon daukar matakin gaggawa da jami’an tsaro suka yi.

A yayin da yake tabbatar da afkuwar rikicin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu ya bayyana cewa, tun farkon lamarin jami’ansu suka yiwa garin kawanya, inda suka kwantar da rikicin.

Exit mobile version