Daga Lawal Umar Tilde Jos
Rayukan mutane dubu bakai ne aka kiyasta sun salwanta a jerin rikice-rikicen da aka yi a jihar Filato cikin shekaru goma da suka gabata. Wannan bayanin na kunshe ne a cikin jawabin da Daraktan Cibiyar inganta zaman lafiya na jihar {Plateau State Peace Building Agency}, Joseph Lengmang, a lolkacin da yake bude taron da Majalisar Kiristoci na Nijeriya, na shekarar 2017. da ta gudanar a Jos fadar gwamnatin jihar a makon da ya gabata, ya ce, ban da duban mutanen da aka raba su da muhallinsu, da lalata dukiyoyin gwamnati da na al’umma na biliyoyin Naira, ya ce, ya nuna har yanzun nan akwai zullumi da fargaba a zukatun wadanda rikicin ya shafa kai tsaye da wadanda akayi rikicin a gabansu, da wandanda ’yan ta adda suka yi ta kai masu hare- hare, a jihar.
Daraktan wanda ya nuna jin takaicinsa bisa ganin a daidai da jihar take shagulgulan murnar samun ingantaccen zaman lafiya na tsawon shekaru biyu, sai kuma kwatsam aka sake samun wadansu jerin tashe-tashen hankula a cikin jihar a ’yan kwanakinnnan da suka gabata kuma ya bukaci al’ummar jihaar da su hada kansu domin surika gudanar da tarurrukan tattaunawa a tsakaninsu ya ce, hakan shi ne mafi dacewa wajen samun hanyar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar da kasa baki daya.