Rayuwar Al’umma Ke Gabanmu Ba Tara Abin Duniya Ba -Inji Walin Hunkuyi

Al'umma

Alhaji ABUBAKAR WALIN HUNKUYI shi ne kuma Makaman Tukuran Zazzau kuma yana daya daga cikin ‘yan takarar kujerar shugabancin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, wakilinmu IDRIS UMAR ZARIYA ya zanta da shi bayan ya siyo Fom na tsayawarsa takarar shugabancin karamar hukuma ga yadda hirar tasu ta kasance.

Ranka ya dade masu karatu za su so su ji sunanka da matsayinka a wannan karamar hukuma

To sunana Alhaji Abubakar Walin Hunkuyi Makaman Tukuran Zazzau

To ranka ya dade ko zaka bayyanawa al’umma dalilin fotowarka takarar kujerar karamar hukumar Kudan a halin yanzu?

To a gaskiya bani na kawo kainaba jama’ar karamar hukumar musamman ma matasa wanda nake tare dasu  sune suka ga ya kamata in fito takarar kujerar karamar hukumar Kudan don in wakilcesu, kuma hakan bai rasa alaka da zaman mutunci da mukayi dasu ba a lokacin baya da kuma yanzu.

To a tunaninka me yajanyo hankalinsu har suka sanyaka a wannan matsayin duk da cewa akwai mutane da yawa a karamar hukumar?

Farko dai dama ni malamin makaranta ne na soma aiki tun a karamar hukumar Ikara, 1985 a matsayin malamin makaranta kuma har sai da na kai matsayi na Headmaster, na zo ma na zama Superbisory Headmaster, bayan nan daga Ikara na dawo Makarfi, daga Makarfi na dawo Kudan Local Gobernment daga nan kuma na koma wani shashe wanda ya ke na ma’aikatar gona domin samu in bautama jama’a na. Daga nan na soma daga mataimakin Superintendent daga nan tafiya tayi tafiya har na kai matsayin mataimakin Director a ma’aikatar gona wanda ya ke kula da malaman gona da kuma ainihin harkar da ta shafi shuke-shuke da irinsu dai abubuwan da suka shafi gona. To ina cikin wannan tsarin ne hankalina ke nuna mini cewa yayin duk da ka dasa matashi to kamar ka gina gari ne, wanda wannan ya sa duk wani matashin da na ji yana neman Admission ko ABU, ko FCE ko Polytechnic ko jami’o’in da suke kusa da mu Kano ne, ko Sokoto, da kuma jami’o’in da suke koyar da harkar kiwon lafiya na kan yi dagaske in ga cewa daluban mu sun samu gurbin karatu a irin wadannan gurin. Wasu da kansu sukan iya biyan kudin registration wasu kuma sai na shiga ciki wanda bansan iyaka ba da dan gudummuwan da na ke da shi. Wannan abin ya sa da yawa matasa na sa su farin ciki da nuna tunanin cewa lallai in na fito na yi jagoranci, na yi shugabanci suna tunanin to lallai za su samu sauki. Yawancinsu in suka gama mukan kafa kuma wajen neman aiki, matashi da yawa wanda bansan iyakarsu ba wanda ya ke Allah ne Ya basu aiki kuma Allah ne Ya yi gudummuwa a gareni ya zamanto a dalilina ya zamanto silan wanda suka samu ayyuka wanda a yau suna iya ciyar da iyalansu da makwaftansu domin mu rayuwar jama’armu shike cikin zuciyarmu ba tara abin duniya ba.

Ranka ya dade akwai kalubale a karamar hukumar Kudan, idan Allah Ta’ala Ya sa ka samu nasara wannan kujerar me zaka fuskanta a gabanka ?

To alhamdulillahi, da farko dai zan yi kokari bisa harkar tsaro. Don in ba tsaro to abubuwa da yawa sukan tabarbare, ba ma a karamar hukumar ba a kasar nan baki daya, in aka samu tsaro to ka ga daluban da muke kokari su zama suma shuwagabanni ne su zama wani abu to zai kasance ainihin sun samu kwanciyar hankali ba wani wanda zai tsoratar da su, ko ba gaskiya ba? Haka kuma manomanmu da suke fita bayan gari suna noma domin samun ingantaccen abinci ga al’umma inda tsaro ka ga ainihin nan ma.za a samu saukin gonan nan cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba. Haka kuma kiwon lafiya, suma malaman kiwon lafiya da yake malamai ne kamar malaman gona ko’ina kowanne lungu za ka ga asibiti za ka ga cibiya na bada magani to suma inda tsaron nan za su shiga wuraren nan su duba mata ne masu maganar haihuwa, jarirai ne don inganta lafiyarsu, don haka dai zan ba tsaro mafificin ainihin al’amari. Sannan kuma sashen ilimi, zan tsaya in ga sashen ilimi ya nagartu, sannan tsaurarawa wajen duba cewa lallai ana ba yara ingantaccen i link domin ilimin nan shine zai sa ainihin a samu natsuwa domin in ka bar mutane ainihin kara zube ba ilimi akwai matsala saboda mutum zai yi abubuwa ne wanda ya ke tamkar bai sai maye ke faruwa ba. In kuwa da ilimi ya san abu kaza da kyau abu kaza ba kyau, to ka ga wannan alhamdulillahi za mu ba ilimi gaskiya karfi da fifiko shima wajen gudanar da shi a karamar hukuma. Sannan bangaren lafiya shima za mu tsaya tsayin daka mu ga shima asibitocinmu ya kasance malaman asibiti suna yin aiki kamar yadda ya dace. Ya zamana ana samun zuwan su malaman asibitin da kuma kyautatawa, da kuma tunanin ainihin su bangaren magunguna ana samun ingantattu, ana samun wandanda za su ruka bincika magungunan da basuyi edpire ba, don sau da yawa za ka ga wasu chemist-chemist ana sayar da magunguna wanda suke sun ruga sun yi edpire kuma a zo ana ba mutane ka ga wannan shi kan shi ma zai iya zama illa ga mutanenmu, so za mu sa ido za mu sa masu ruwa da tsaki a harkar ilimin kiwon lafiya wajen jagorancin tsaftace karamar hukumar mu da duba abubuwan da suka dace.

To Rankaya dade a irin wadannan lokutan mukan so mu ji ra’ayinku ga matasa musamman yayin da ake gudanar da zabe na cikin gida da na waje, wane shawara za ka baiwa matasa don ayi lafiya an gama lafiya?

To ina kira ga matasa cewa duk inda suke lungu-lungu daga karamar hukumar mu ta kudan daga kuma kowacce mazaba ne dan Allah don Annabi su tsaya su bi doka da oda, su zauna lafiya da ‘yan uwansu. Siyasa ra’ayice, koda kana son Alhaji Abubakar Wali Hunkuyi Makaman Tukuran Zazzau to kar ka yarda a saboda shi ka je kana fada a kan cewa dole sai an yi ne. Ni ba na fito ne ko in yi ko in mutu ba na fito ne da yardar Allah, in na rasa wallahi farinciki zan yi domin Allah ne Ya ga cewa rasawar da na yi shine mafi kyau, in kuma na samu to shima nan murna zan yi don shine cewa ba mamaki Allah Ya ga cewa samuna shine mafi kyau. Don kullun ko a wajen hidima da al’umma na kan gayawa al’umma su samu cikin addu’a in zamu zamo alkhairi akan mulkinsu a wannan karamar hukuma tamu mai albarka to Allah Ya bamu, in kuma ba mune alkhairi ba Allah Ya kawo wanda zai fi zama alkhairi mu taru da ni da shi magoya bayana mu bi shi ya kasance ainihin karamar hukumar mu ta zauna lafiya zama na kwanciyar hankali da lumana a zauna Colin mutunci.

Ranka ya dade daga karshe abinda na manta shine da yawa yan takar kan bugs Costa amma basu da Samar siyan fom lamarin nasu zai ya zama dodorado to ya naka lamarin yake?

Ina cikin na farko a karamar hukumar Kudan a wajan sayan form na takarar neman kujerar Chairman, kuma a yanzu haka ma za ka ganshi gashi nan a hannuna ina kokarin cikewa ne in tasa jama’a na mu je mu mayar da wannan form duk ka’idojin da ake bi na takara muna kiyayewa mun fito bisa ga yardar Allah zamu kiyaye mutuncin jama’a, zamu kiyaye mutuncin mu domin  kasata Nijeriya, da jihata jihar Kaduna, wanda su nake alfahari da su da karamar hukumata mai albarka

To a karshe kanada wani sako ga jama’ar karamar hukumar ta Kudan Wanda baka fadiba a baya?

Sakona shine nasan karamar kudan sun shiga wani hali mawuyaci don haka duk wanda aka batawa rayuwa to yayi hakuri mu zamu sanyaya masa rayuwa cikin ikon Allah.

Nagode sir, Allah Ya saka da alkhairi

Madallah nima na gode.

Exit mobile version