Connect with us

ADABI

Rayuwar Aurena: Gajeren Labari Daga Amina Lawan (Shalele)

Published

on

Ina jin ana ta cewa rayuwar aure hakuri ce, ban gane ba ban gaskata ba sai da wani al’amari ya faru a kai na. Na san za ku so ku ji dalilin da ya sa na gasgata hakan, za ku samu amsarku ne duk a cikin labarin rayuwar aurena. Sunana Nabeela ina da yayu guda Biyu Bilal da Latifa. Da ni da yayata Latifa mun taso ne kamar kawaye saboda ba tazara sosai tsakaninmu, shekara biyu kawai ta ba ni, muna yawan yin fada saboda ni din marar ji ce ita kuma natsattsace ina son gayu ina tafiya da zamani ita kuma ba ta damu da duniya ba. Ta na rayuwa ne a kan tsarinta. Ni mace ce mai sakin fuska mai raha ga kowa hakan ya sa min farin jini, ita kuwa Latifa ba ta da sakin fuska  kuma ba ta saurin sakin jiki da mutane. Wanda ya girme ta ta na girmama shi, wanda ta girma kuwa ba ta kula shi, tsaranta kuma ta na kama kanta sosai.

Ta na so na sosai amma duk da haka muna samun sabani, a cikin raha zan bata mata rai har ta yi fushi, duk da haka zan ta bin ta ina mata abun dariya har ta sauko. Mun shaku sosai da ita. Ta gama karatun sakandare da shekara daya sannan ni ma na gama. Lokacin ne na hadu da Adam yana da kyau sosai sai dai halin ba daya ba, don shi bai da sakin fuska, ba ya yawaita surutu, son da ya ke nuna min ya sa na mallaka masa zuciyata na zabe shi a matsayin mijin da zan aura. Ita ma yayata Latifa ta samu wanda take so aka daura mana aure rana daya aka kai ta Kaduna ni kuwa ina kano.

Bayan aure muka kara shakuwa sosai da ita dandanan ta kira ni ta ji lafiyata. Mijina ko ba ya surutu da ni, ba ya sakar min fuska sai na ji ni a takure kasancewa ta mai son fara’a shi ya sa in na samu na fita unguwa ina jin dadi sosai kafin in dawo gida. Ana haka na samu ciki ita kuwa yayata Allah bai kawo ba dandanan ta kira ta ji lafiyata da ta cikina. Har na haihu na samu mace aka sa mata Muhibbat. Tunda na haihu take yawan kawo min ziyara don duba Muhibbat, takan yo mata dinkuna masu kyau kasancewar ta mai dinki hakan na mini dadi sosai.

Ni kuwa bana zuwa ko’ina bana sana’ar komi, Adam ba ya son sana’a, ba ya barin fita unguwa, ba ya kuma ba ni kudinshi, dama can ban ci kudinsa ba ina son sa ne ba dan kudinsa ba saboda Allah. Duk lokacin da zan nemi kudi sai mun yi sabani musamman in zan je unguwa ta hawan mota, sai raina ya baci sosai duk da haka ban taba fadawa kowa ba ina biye da shi kuma ina son sa a hakan. Lafiya lau zai shirya ya tafi gaida iyayenshi ni kuwa ba ya tunawa da ni ma ina da iyayen, da na tambaya zai ce bai da kudi dole na hakura.

A na haka yayata ta samu ciki ta haifu yaron bai zo da rai ba, ta yi kuka ta shiga damuwa saboda ta na son haihuwar kuma mijinta na so. Na so zuwa amma bai bar ni ba. Bayan haka sai na samu ciki bayan kwana biyu muna waya nake fada mata tai ta murna ta na min addu’ar sauka lafiya, har ta roke ni in na haihu na ba ta yaron ko na ba ta Muhibbat. Cikin kwantar da kai na ce tai hakuri Adam ba zai bari ba.

Bayan lokaci na haihu na sami namiji aka sa masa sunan uban mijina muna kiransa Muklis. Ba jimawa ta samu ciki muna ta murna, da ya shiga wata Uku ta yi bari. Ba damar tambayar Adam domin zuwa duba ta don kar rayuka su baci haka nai hakuri na yi shiru, sai dai nai ta kiran ta a waya ina jin lafiyarta.

Tun daga nan ba ta kara haihuwa ba ni kuwa ina ta haihuwa har hudu. Sai ta samu ciki lokacin mu kai ta murna daga ni har ita, mijinta ko kamar zai zuba ruwa kasa ya sha don son da ya ke mata har yanzu bai kara aure ba. Tun da ta samu cikin nake yawan kiran ta wani lokaci idan muna waya sai ta rika cewa “Nabila ji nake yi kamar mutuwa zan yi.” Ni kuwa in rika kwantar mata da hankali ina cewa”In sha Allah lafiya za ki haihu.” Ita ko ta rika rokona in rika mata addu’a.

Bayan watanni Tara da tsakar dare ta fara nakuda, mijinta ya kai ta asibiti a gaggauce, ta sha wuya amma haihuwar shiru. Wannan ya sa aka shiga da ita dakin tiyata ta na ta kyarma ta na ciccijewa mijinta Usman hankalinshi ya tashi ya kira gidanmu ya fada musu a cikin daren suka taho asibitin. Bayan awanni Biyu aka fito da ita aka kai ta dakin hutu, lokacin har su mamana sun iso. Mama ta rike ta ta na ta mata sannu.

Ta na hawaye tace “Ku kira min Latifa mutuwa zan yi, ku kira ta in ba ta dana.” Mamarmu na hawaye ta ke ba ta hakuri, amma ta cigaba da kira na idanunta lumshe ta na ta hawaye. Cikin kankanin lokaci jini ya balle mata, a rikice mama ta kira likita suka fara ba ta taimakon gaggawa, aka dora mata jini yana shiga da sauri ya kare aka kara dora mata wani.

Mama ta shigo dakin ta na hawaye anty Latifa idanunta rufe tace “Ku kira min Nabila dan Allah.” Mama ta fita mijinta ya kira mijina kasancewar asuba ta yi ya fada mai an wa yayata aiki kuma ba ta da lafiya sosai. Ina cikin bacci ya tada ni ya ke fada min na fara kuka ina “innalillahi wa inna ilaihi rajiun!” Ya ja tsaki yace “Wanda aka yi wa aiki sai hakuri dama”

Na ce “An ce fa aiki dan Allah ka bar ni in je kar ta mutu ba mu yi bankwana ba.” Yana tsaki yace “Sai ku rika kirawa mutum mutuwa daga ciwo ba kwa nema masa sauki.” Duk yadda na so ya bar ni in gano ta ya ki, yace shi bai da lokacin kai ni kuma bai da kudi in kuma ina da su in tafi don kawai ya san ban da ko sisi. Na cigaba da kuka ina hidimar yara su tafi makaranta kwatsam sai ga waya mamanshi ba ta lafiya a Wudil, jikinshi na rawa ya tafi ni kuwa na tura yarana makaranta sai na tuna akwai makwabciyata ta haihu kila ta na da kudi ta ara min ina zuwa na samu da sauri na kama hanyar Kaduna.

Ina ta kuka a mota Adam ya kona min rai sosai ga rashin lafiyar yayata mutane na ta kallo na, wasu na ba ni hakuri. Muna shiga Kaduna wayata ta dau ruri ina dauka na ji muryar mamata ta na kuka tace “Latifa ta rasu Nabila, ta rasu da son ganin ki.” Na fashe da sabon kuka duk mutanen motar suka dau salati na cigaba da yi yarona na taya ni suka kai ni bakin asibitin suna ta tausaya mini.

Na shiga tashin hankali ganin gawar yayata, ga yaronta yana ta kuka haka muka koma Kano aka yi mata sutura mama ta damka min yaron hannuna saboda cika wasiyyar yayata.

Ina kuka a ka kawo mi ni wayata na ruri, Adam na kira ina dauka ya fara masifa na tafiyata yara sun dawo suna kofar gida. Ban ce komai ba na kashe wayar ina cigaba da kukan rashin yayata. Washe gari shi da yara suka zo gaisuwa, ban san wa ya fada mai rasuwar ba, kallo daya kawai na yi masa ya fita raina har son da nake masa na ji babu shi.

Bayan kwana Bakwai ya zo muka koma Kano ban sani ba ko an fada masa an ba ni yaro amma bai ce komai ba. Na cigaba da kula da yarona da aka sawa Noor, yana da kyau fiye da yarana. Sai kishi ya kama Adam muka rika samun sabani. Wata rana mu kai fada na koma gida muna zuwa iyayena suka fahimci Noor ne matsalar hakan ya sa suka karbe mini shi ina kuka yana kuka, da ni kadai ya saba amma aka raba ni da shi.

Na dawo ina kuka bana jin dadin rayuwata ko kadan an raba ni da dan amana, haka na hakura na cigaba da kula  da yarana da mijina. Lokacin ne na kara gane rayuwar aure duk hakuri ce shi kuwa Noor yana wurin mamata ta na cigaba da kula da shi. Haka na cigaba da rayuwar hakuri da neman lada tare da mijina Adam har zuwa yanzu da nake ba ku labari bai sauya hali ba.

 

Karshe!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: