Rayuwar Kasimu A Industiri: Gwarzon Jarumi Da Ne Bai Taba Tsalle-tsalle Ba

Daga Al-Amin Ciroma

A ranar Lahadi 3 ga Satumbar 2017 ne duniyar finafinai a Nijeriya ta wayi gari cikin alhini da rashin daya daga cikin fitattu kuma jigajigai a fannin wasannin kwaikwayo. Marigayi Kasimu Yero, wanda ya rasu yana da kimamin shekaru 70 a duniya, ya taka muhimman matsayai a duniyar finafinai, ba ma ta Hausa kadai ba, hatta a fannin Turanci ba a yi masa rata ba.

Marigayi Alhaji Kasimu Yero ya sami manyan lambobin yabo na kasa har guda biyu na farko a zamanin Tsohon Shugaba Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekarar 1989, inda tsohon shugaban ya ba shi lambar girmamawa ta MFR, ya kuma kara samun wata lambar yabon MON har ila yau a shekarar 2001, lokacin mulkin Tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo. Mutum ne da za a fassara shi a matsayin kwararre ta kowace fuska a fagen shirye-shiryen wasannin kwaikwayo.

Tauraruwarsa ta fara haskawa kusan tun a ranar da ya fara shiga fagen masa’anatar wasannin kwaikwayo, wanda idan za a iya tunawa tun a shekarun 1980, lokacin da yake fitowa a shirye -shiryen kafar yada labarai ta kasar wato NTA – a wasannin ‘Karambana’, ‘Magana Jari Ce’ (na Hausa da na Turanci) da dai sauransu, kusan babu kamar sa a cikin dukkanin sa’oinsa.

Masana da masu fashin bakin harkokin finafinai baki dayansu sun tafi a kan cewa Marigayi Kasimu ya kasance cikakken dan wasa, wanda bai taba bayyana maitarsa na son tara dukiya ko babakere da handama ba. A yayin da masa’antar ta cika ta batse da ‘yan mu-ci-barkatai, ma’ana a sami mutum daya, yana hada ayyukan mutane goma a kansa, shi kuwa Marigayi Kasimu, bai taba sha’awar hakan ba.

Ya gwada wa jama’a musamman masoyansa cewa shi dai dan wasa ne, ma’ana jarumi ne mai fitowa a cikin wasannin kwaikwayo da finafinai. Amma ba kamar yadda a yanzu ake samun dan wasa ya fito a matsayin furodusa, darakta, mai koyar da rawa, marubucin labarin fim din sannan har ila yau ya zama shi ne dan kasuwan da zai yi tallata fim dinsa don shiga kasuwa. Wannan a kaikaice ba karamin nakasu ba ne ga masa’antar ba. A duniyar kirkira da fasaha, masana sun bayyana cewa muddin ana muradin ciyar da masana’antar fim gaba, tilas a bude kofar ba wa masu fasaha damar shiga don baje kolinsu.

Shi dai Marigayi Alhaji Kasimu Yero ya amintar da kansa daga irin wannan ‘yan handama da babakere. Ya yarda cewa a ba wa kowa damar baje kolin abin da Allah Ya huwace masa. Na taba samun damar zantawa da shi a gidansa dake shiyyar Marafa a Kaduna. Bayan da muka gama tattaunawa da shi, sai na yi masa wata tambayar daga ni sai shi. Na ce, ‘Ranka ya dade, a daidai lokacin da kannenka da yaranka suke ci gaba da samun tagomashi cikin industry ta fannoni da dama, yaya ba ka yi niyyar zama gogarman darakta ba, tun da kun ga jiya, kun ga yau…’

Jin haka, sai ya yi dariya. Ya ce, ‘Me ya sa ba ka ce da ni in shiga harkar jarida na zama edita ba?’ A nan zancen ya kare! Marigayi ya ce da ni, muddin so ake a samu bunkasar tattalin arziki da ciyar da masana’anta gaba, tilas kowa ya tsaya a matsayinsa. Ya kara da cewa idan mutum ya tafi Amurka zai yi wahala ka ga mutum daya yana gwama ayyukan mutane da dama, sannan ya yi zaton aikin zai zama na kwarai. Allahu Akbar! Allah Ya jikan Kasimu, Ya gafarta masa, Ya kuma yafe masa kurakuransa, amin.

An dai yi jana’izar marigayin a Kaduna a ranar Lahadi kamar yadda addinin Musulunci ya shimfida. Shugaba Muhammadu Buhari yana daga cikin wadanda suka nuna jimami da alhinin rasuwar wannan jarumi, inda ya fassara marigayin a matsayin fitaccen jarumi mai dimbin fasaha a zamaninsa. Shugaban ya aike sakon ne ta hannun Ministan Watsa Labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammed, inda ya ce Kasimu Yero a matsayin fitaccen jarumin da ya zama babbar katanga ga masana’antar finafinai a Nijeriya.

A daidai lokacin ake ci gaba da jimamin rasuwar wannan gogarma a fagen fim, haka ma kwararru ke fatan ganin wadanda za su sa takalmin Marigayi Yero. Kwararrun na kafa hujjar ganin yadda wannan fitacce yake tafiyar da harkokinsa a lokacin da aka gayyace shi ‘Lokeshin’ wato dandalin shirya wasannin kwaikwayo ko finafinai. Babban abin dubawa shi ne yadda yake ba wa kowa ladabi da sanin aikin da aka ba shi.

Zan iya tunawa a lokacin da muka shirya wani fim da shi mai suna ‘Aure ko Boko’ a shekarar 1998. A wannan lokacin ma iya cewa Marigayin yana cikin ganiyarsa matuka. Kuma ni ban taba haduwa da shi ido da ido ba sai a lokacin. Na rika saka yadda zan gan shi. Amma abin mamaki, ko da ya zo inda za a dauki shirin. Sai na gan shi kamar ba shi ba. Komawa ya yi gefe, inda ‘yan kananan jarumai ke zama, bai nuna kyama ko jin kansa a matsayin fitacce ba. Sannan ya gaida kowa cikin fara’a da murmushi, kana ya zauna tare da su.

Ba ma wannan ne zai ba ka sha’awa da marigayin ba, ba za ka ji shi yana surutu ko shiga abin da ba a sa shi ba. Sai ma ka dauka ba ya magana ko kuma bai iya magana ba. Amma a daidai lokacin da darakta zai ce masa ‘Action’ ma’ana a lokacin da za a fara, nan ne za ka sha mamaki.

Tabbas fafajiyar shirin fim na duniya ta yi babban rashin gwarzo, jarumi, fitacce mai cike da fasaha da basira. Har ya komawa Mahaliccinsa, Kasimu bai taba raina na kasa da shi ba, ballanta ya muzanta na sama da shi. Komin kankantar furodusa idan ya zo neman ya taka wata rawa a fim dinsa, farko zai nemi ‘Script’ wato labarin fim din ya duba. Idan da gyara zai bayar da shawara, sannan ya je ba tare da tunanin ya fi kowa ba. Alhali a fagen fim din nan dai, ya fi kowa!

Jarumai da dama a cikin masa’antar fim a Arewa sun bayyana alhini da ta’aziyyarsu. Farko a wannan sahun shi ne Malam Sani Mu’azu, wato Tsohon Shugaban Kungiyar MOPPAN ta kasa, wanda ya bayyana Kasimu a matsayin bango abin jingina a harkar finafinan Hausa. Malam Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na ‘Facebook.’ Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikansa, Ya kuma albarkaci bayansa.

Shi ma a nasa shafin sadarwar ‘Instagram’ fitaccen jarumi Ali Nuhu ya yi fatan Allah Ya jikan Alhaji Kasimu Yero, ya kuma fatan makusantansa da su kara jimurin wannan babban rashi.

Hakika rasuwar ta Kasimu ta girgiza ilahirin duniyar finafinai, inda Hajiya Hajara Usman, wadda aka fi sani da Mama Hajjo, wadda suka sha yin fim tare da marigayin ta ce marigayi Kasimu ya dauke ta kamar ’yarsa saboda mutunci da girmamawa. Ta yi addu’ar Allah Ya yafe masa kurakuransa, Ya kuma kai haske kabarinsa.

A yayin da yake nasa ta’aziyyar Jarumi, Furodusa kuma Darakta Falalu Dorayi, wanda suka taba yin aiki tare ya bayyana cewa zai yi wahala a samu wanda zai maye gurbin marigayin. Ya yi addu’ar Allah Ta’ala Ya jikansa da gafara amin.

Ta’aziyyar wannan gogarma ba abin da za a yi shi a zama guda ba, saboda yanayin ficensa da yadda ya dauki sana’arsa a matsayin abin tinkaho. Abin ya fi kamata a mayar da hankali dai shi ne, wane ne zai sanya takalmin da ya bari?

Idan har aka yi la’akari da dan gabatarwar da na yi a farkon wannan makala, za a fahimci cewa Kasimu Yero mutum ne fitacce, wanda ya sami damar fahimtar kansa, sannan ya taka muhimmiyar rawar ganin ba a yi masa rata a kan dukkanin harkokinsa a masana’antar fim ba. Karamin misali a nan shi ne, a lokacin da ake gabatar da shirin ‘Cock Crow At Dawn’ a shekarun 1980, marigayin ya fito a matsayin ‘Uncle Gaga.’ Mai kallo zai rantse cewa ba shi da alaka da Hausawa saboda irin yadda ya mayar da kansa daidai da labarin da darakta ya ba shi.

Irin wadannan baiwa da basirar da Allah Ya ba shi, suka sa ake ganin zai yi matukar wahala a sami wanda zai tsaya ya jajirce har ya kai matsayin da ya taka a rayuwarsa. Duk kuwa da cewa ba tilas sai ka zama wani ba, amma kwarewarsa, basira, ladabi da biyayyarsa a farfajiyar finafinai a Nijeriya ba abin yarwa ba ne. Ya dai kamata jarumai masu tasowa su rika bibiyar halayensa.

Jarumi ne da ya tsaya kai da fata wajen fito da kyawawan al’adunmu na Arewa da kuma cikakken tarbiyyar gidan sarautar Sarakunan Arewa. Kasimu ya kasance kalilan daga cikin wadanda suka yi tsayin daka wajen nunawa takwarorinmu na Kudu cewa masarautun Arewa cike suke da ladubba daban-daban da kayatattun al’amurra. Duk wadannan ya yi su a cikin finafinan da ya yi na Hausa da Turanci.

Marigayin ya bar duniya a ranar 3 ga Satumba, 2017. Ya rasu ya bar ‘ya’ya takwas da jikoki 10, Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa kurakuransa, Ya albarkaci zuri’arsa, amin.

Exit mobile version