Rayuwar Mambobinmu Na Cikin Hatsari A Nijeriya – IPOB

IPOB

Daga Khalid Idris Doya,

Kungiyar nan da ke gwagwarmayar neman kafa yankin Biafra wato (IPOB) ta yi yekuwar zargin cewa mambobinta su na cikin mummunar hatsari bisa barazanar da suke zargin jami’an tsaron Nijeriya ke musu.

Kungiyar ta ce, wasu daga cikin mambobinta an sanya alami a kansu, wasu kuma ana cigaba da farautarsu daga hannun jami’an tsaron Nijeriya.

A sanarwar manema labarai da sakataren watsa labaran kungiyar Emma Powerful, ya fitar, IPOB ta kara da cewa, irin barazanar da ake yi musu ya sanya wasu a bisa tilas suka bar Nijeriya zuwa wasu kasashe yayin da wasu kuma suke fuskantar neman kamu da azaftarwa.

Kungiyar ta nuna damuwarta a bisa cewa wadanda suka bar kasar nan bisa dole suna cikin damuwa mai tsanani a bisa rashin samun damar kawo ziyara gidajensu da garuruwansu ko halastar bikin bison mamata daga makusantansu ko masoyansu dukka bisa fargabar kamu ko daurin jami’an tsaro.

Sanarwar ta ce, “Mu mambobin kungiyar IPOB ne wanda muke karkashin jagorancin Mazi Nnamdi Kanu, muna sanar da duniya cewa su sani rayuwar mambobinmu na cikin tsananin hatsari da fargaba a Nijeriya. An sanya yi makin din wasu mambobinmu a yayin da wasu kuma jami’an tsaron Nijeriya na kan farautarsu ruwa a jallo.

“Wasu mambobimu sun samu arcewa daga Nijeriya zuwa wasu kasashen domin tsira da rayukansu daga kamu da azaftarwa. Su ma wadanda suka bar Nijeriya din suna cikin damuwa da fargaba na rashin samun damar ziyarar ‘yan uwansu da abokan arzikinsu.

Kungiyar daga nan kuma sai ta jinjina wa kungiyoyin kasashen waje da suke baiwa mambobinta wuraren zama, sun roki sauran kasashen su ma su yi kokarin hakan.

Exit mobile version