Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Rayuwar Nana Khadija Da Gudunmawarta Wajen Yada Addinin Musulunci (IB)

by
2 years ago
in TARIHI
6 min read
Rayuwan Sayyadina Abubakar Da Ayyukansa Na Yaxa Addinin Musulunci (III)
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Cigaba daga inda muka tsaya a makon jiya.

Khaulah ‘yar Hakim ta zo wajen Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) tace. “Ya Manzo Allah! Shin ba za ka yi aure ba?” Sai ya ce. “Wa zan aura?” Sai tace. “Idan ka ga dama budurwa, idan ka ga dama bazawara.” Sai ya ce. “Wace ce budurwar? Kuma wace ce bazawarar?” Sai tace. “Amma bazawarar ita ce Saudatu ‘yar Zam’ah, amma budurwar ita ce ‘yar mafi soyuwa a gare ka, Aishah ‘yar Abubakar Assiddik (R.A.).”

Sai ya ce. “To ki gaya masa ina neman auren ‘yar sa.” Sai taje wajen Sayyadina Abubakar ta gaya masa, mutane sun kasance a Jahiliyya basa aurar ‘yar dan uwan su (Babban abokin su) saboda ‘yan uwan taka. Sai Sayyadina Abubakar ya ce. “Shin hakan zai yiwu kuwa? Ita fa ‘yar dan uwan sace?” Sai ta koma wajen Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) sai ta gaya masa abin da ya fada. Sai ya ce. “Kije kice da shi, shi dan uwana ne a addini, kuma ita ta halatta a gareni na aure ta.”

Labarai Masu Nasaba

Tarihin Kafuwar Masarautar Nupe Da Jerin Sarakunanta

Tsarin Shugabancin Hausa/Fulani Gabanin Zuwan Bature

Da Sayyadina Abubakar yasan haka, sai ya yarda. Uwar muminai Nana Aishah ta kasance an bawa Jubair dan Mud’im dan Adiyyi ita, sai Sayyadina Abubakar ya shiga damuwa, saboda saba alkawarin da zai yi saboda bai tuntube shi ba, sai ya hadu da Mud’im dan Adiyyi (Mahaifin Jubair), sai Mud’im ya juya ya ce da Matar sa mai zaki ce (akan batun auren Aishah da dan mu)?

Sai ta ce da shi, ya kai dan Abu Kuhafah! Mun fasa, domin idan ka aurawa dan mu aure da ‘yar ka, to za ka shigar da shi addinin ka.

Sadar da Zumuncin Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) Ga Kawayen Uwar Muminai Nana Khadija Bayan Rasuwarta

Nana Khadijah (Allah ya kara mata yarda) ta rasu sai dai bata rasu a zuciyar sa ba, domin Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya kasance yana yawan ambaton Uwar Mumina Nana Khadijah, saboda girman da take da shi a zuciyarsa, ba’asan ya yi bakin cikin mutuwar wani sosai ba, sama da yadda ya yi akan mutuwar Nana Khadijah, kuma bai jima yana ambaton wani wanda ya mutu ba, sama da yadda ya jima yana ambaton Nana Khadija.

Anas ya rawaito cewa, Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya kasance idan an zo masa da wani abu yana cewa. “Ku tafi da shi wajen wan ce, domin hakika ita kawar Khadijah ce.”

An karbo daga Uwar muminai Nana Aishah (Allah ya kara mata yarda) tace, wata tsohuwa ta zo wajen Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) alhalin yana wajena, sai Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya ce mata. “Wace ce ke?” sai tace. “Juththamah Almuzaniyyah.” Sai ya ce. “A’a, kece Hassanah Almuzaniyyah, ya ya kuke, ya ya halinku? Ya ya kuka kasance bayan rabuwar mu?”

Sai ta ce, “Mun kasance cikin alheri na bada fansar mahaifina da mahaifiyata gare ka ya Manzon Allah.” Da ta fita sai nace. “Ya Manzon Allah! ya naga kana irin wannan tarba ga wannan tsohuwar ne?” Sai ya ce. “Hakika ita ta kasance ta na zuwa mana a lokacin Khadijah, hakika kyakkyawan cika alkawari yana daga cikin Imani.”

Kuma idan kaso idanuwan ka zasu cika da hawaye saboda tausayin Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) lokacin da yaga wata sarkar Nana Khadijah bayan rasuwarta da dogon lokaci.

An sake karbo haidisi daga Uwar mumina Nana Aishah matar Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) tace. “Lokacin da mutanen Makkah suka turo da abin da zasu fanshi mutanen su wadanda aka kama a yaki, sai Zainab ‘yar Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) ta aiko da dukiya domin fansar mijin ta Abul Ass Dan Arrabi’u, sai ta aiko da wata sarkar ta wacce Nana Khadijah ta bata lokacin data tare a gidan Abus Ass.” tace da Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya ga sarkan, sai yaji tausayin ta sosai, sannan ya ce. “Idan kunga za ku iya sakar mata mijinta ku mayar mata sarkar ta, toku aikata.” Sai suka ce. “Zamu aikata hakan ya Manzon Allah, sai suka sake shi, suka mayar mata da sarkar ta.”

Falalar Uwar Muminai Nana Khadija Imamuz Zahabi ya ce. “Falalar ta tana da yawa, tana daga cikin wadanda suka cika, ta kasance mai hankali mai girma mai kiyayewa mai karamci, ‘yar aljanna, Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya kasance yana yawan yabon ta, yana fifita ta akan ragowar iyayen muminai, yana zuwa makura wajen girmama ta, har uwar muminai Nana Aishah ta ce. “Ban yi kishi ga wata mata ba, kamar yadda nayi kishi da Khadijah, saboda yadda Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) yake yawan ambaton ta.” Tace: “ya aure ni a bayan ta da shekara uku.”

”Yana daga cikin matsayin ta shi ne Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) bai auri wata mata ba sai bayan ta, duk kusan ‘ya’yan sa ita ta haife su, haka nan bai rike baiwa ba, sai bayan ta rasu, ya yi bakin cikin rabuwa da ita, ta kasance cikakkiyar abokiyar zama, ta kasance tana ciyar da dukiyar ta, Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya kasance yana yin kasuwanci da dukiyar ta, hakika Allah ya umarce shi da ya yi mata bushara da gida a aljanna na azurfa, babu hayaniya a cikin sa babu wahala kuma.

Falalar Da Uwar Muminai Nana Khadija Ta Kebanta Da Ita:

Uwar muminai Nana Khadijah tana da falalolin da suka kebance ta sama da ragowar matan Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam), daga cikin su:1. Ita ce farkon matan Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam).2. Bai auri wata mata ba sai bayan ta, duk kusan ‘ya’yan sa ita ta haife su, haka nan bai rike baiwa ba.3. Kuma mafi soyuwa a wajen sa, yana kuma kirga son sa gare ta arziki ne daga Allah. Uwar muminai Nana Aishah tace. “Banyi kishi da wata mata ba, sama da yadda nayi kishi da Khadijah, ta rasu kafin (Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya aure ni, saboda ina ji yana yawan ambaton ta, kuma Allah ya umarce shi da ya yi mata bushara da gida a aljanna na azurfa, kuma wani lokaci ya kasance yana yanka Akuya sai ya kyautar ga kawayen Khadijah abin da zai ishe su.”

  1. Hakika ita ce mafi alkhairin matan wannan al’umma. An karbo hadisi daga Aliyu Dan Abu Dalib (Allah ya girmama fuskarsa) ya ce. Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya ce. “Mafi alkhairin mata ita ce Maryam, mafi alkhairin mata ita ce Khadijah.”5. Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya kasance yana yawan ambaton ta, da sadar da zumuncin ta bayan rasuwar ta, kamar yadda ya gabata.6. Hakika Mala’ika Jibrilu ya yi mata bushara da cewa Allah yana gaishe ta, kuma shi ma yana gaishe ta, ya yi mata albishir da gida a aljanna. An karbo hadisi daga Abu Hurairah (Allah ya kara masa yarda) ya ce. Jibrilu ya zo wajen Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam), ya ce, “Ya Manzon Allah! wannan Khadijah ce, hakika zata zo a tare da ita da akwai kwano da akwai miya ko abinci ko abin sha, idan tazo maka to kayi mata sallama daga Ubangijin ta, da kuma gare ni, sannan kayi mata bushara da gida a aljanna na azurfa, babu hayaniya a cikin sa babu wahala kuma.” Malamai sun bayyana cewa Nana Khadijah tafi duk matan wannan al’umma falala, kai har ma ta fi Uwar Mumina Nana Aishah falala. Dan Hajar ya ce. “Suhaili ya ce, Abubakar Dan Dawud ya kafa hujja da wannan hadisi akan cewa Nana Khadijah ta fi Nana Aishah falala, saboda Nana Aishah Jibrilu ne ya gaishe ta da kan sa, amma Nana Khadijah ya isar mata da gaisuwar Ubangijin ta ne.”7. Hakika ita tana daga cikin farkon shiga musulunci, ita ce farkon wacce ta fara imani da abin da Allah ya saukar, domin haka tana da ladan ta, da ladan wanda ya musulunta a bayan ta.8. Bai aura mata kishiya ba har tabar duniya, ta kebanta da shi shekara goma sha uku ita kadai, daga rayuwar sa ta aure, kenan ta albarkaci wajen daya cikin uku na rayuwar sa kenan.9. Son da Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) yake yi mata, soyayya ce daga Allah wacce ya azurta shi da ita.10. Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya ce. “Ba don kariya ta Abu Dalib ba, da kuma dukiyar Khadijah da takobin Ali ba, da wannan addini bai tsaya da kafarsa ba.” (Musulunci ya tsaya da kafarsa ne saboda kariya irinta Abu Dalib, dukiyar Khadijah da kuma takobin Sayyadina Ali (AS). Domin Karin bayani akan abin da ya gabata akan uwar muminai Nana Khadija sai a duba: Ahzab (32). Fat’hul bariy (7/134). Assiyar (2/111). Arrahiykul makhtum (1/46). Bukhari a Al’adbul mufrad (1/90). Almustadrak (1/15-16). Ahmad (26362), (6/212). Fat’hul bari (7/103). Al’istiy’ab (2/775). Al’isabah (8/347). Suratul alak (1-3). Assirah (1/236). Fat’hul bari (7/100). Al’isabah (8/102). Bukhari (320, 2435, 3815, 3818, 5081). Assiyar (2/110). Da wannan mu ka zo karshen tarihin rayuwar Uwar Muminai Nana Khadija da gudunmawarta wajen yada addinin Musulunci. Sai wani makon mai zuwa za ku ji mu da tarihin daya daga cikin iyayyen muminan.

Daga dan uwanku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri, 08098331260.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Kwararru Sun Ce Akwai Jan Aiki A Fannin Noman Nijeriya

Next Post

Sabuwar Cuta Mai Tsanani Ta Bulla A Habasha

Labarai Masu Nasaba

Masarautar Nupe

Tarihin Kafuwar Masarautar Nupe Da Jerin Sarakunanta

by
8 months ago
0

...

Hausa/Fulani

Tsarin Shugabancin Hausa/Fulani Gabanin Zuwan Bature

by
9 months ago
0

...

Coomassie

Tarihin Tsohon Sifeta Janar Na ‘Yan Sanda Ibrahim Coomassie

by
10 months ago
0

...

Mai Martaba Aminu Ado Bayero: Sarkin Kano Na 15 A Daular Fulani

Mai Martaba Aminu Ado Bayero: Sarkin Kano Na 15 A Daular Fulani

by
11 months ago
0

...

Next Post

Sabuwar Cuta Mai Tsanani Ta Bulla A Habasha

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: