Rayuwar Sarkin Zazzau Alheri Ne Ga ’Yan Nijeriya -Alhaji Ali Ba-Kware

 

An bayyana rayuwar mai martaba Sarkin Zazzzau Alhaji Shehu Idris a matsayin Sarkin Zazzau shekara 43 da suka gabata da cewar, alheri ne ga duk wani dan Nijeriya, musamman in an dubi yadda yak e bayar da gudunmuwarsa na tabbatar zaman lafiya a shekarun day a yi a karagar Zazzau.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin tsohon shugaban ‘yan kasuwar takin zamani da ke P/Z a zariya, a lokacin day a zanta da wakilinmu kan cikar sarkin Zazzau shekara 43 da nada shi Sarkin Zazzau a shekara ta 1975.

Alhaji Ali Ba-Kware ya ci gaba cewar, babu ko shakka duk wanda ya ke saurarorn jawaban mai martaba sarkin Zazzau, zai yadda cewar, babu abin da ya sa a gabansa kamar batun zaman lafiya, da in ya samu, daga nan ne za a sami duk wani ci gaban da ake bukata.

Wannan batu na zaman lafiya da Mai martaba sarkin Zazzau ya sa a gabansa shekara 43 da suka gabata, al’ummomin wasu jihohi ma sun amfana, musamman in an tuna, a cewar Alhaji Ali Ba-kware, a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, mai martaba sarkin Zazzau ya jagoranci kwamitin tabbatar da zaman lafiya a Yelwan Shandam, wanda wannan kwamiti, shugaban kasa Obasanjo ya kafa.

Kuma tun kammala aikin da aka dora wa wannan kwamiti, batun duk wata tashin-tashina ta zama tarihi a daukacin yankin Yelwan Shandam, da sauran garuruwa da suke kusa da wannan gari da aka dade ana yin fadace-fadacen kabilanci, matsalolin suka zama tarihi har zuwa yau.

Alhaji Ba-Kware ya yi amfani da wannan daman a zantawa da wakilinmu, inda ya yi kira ga gwamnatin tarayyar Nijeriya, da karshen wannan shekara ta 2018, ta sa sunan mai martaba Sarkin Zazzau a cikin jerin sunayen wadanda za a bas u lambar girmama ta kasa, a ba shi lamban yabo, kan gudunmuwar day a ke bayarwa, domin ci gaban ‘yan Nijeriya da kuma Nijeriya kan ta.

Da kuma Alhaji Ali Ba-kware ya juya ga batun matsalolin tashin-tashinar da ke faruwa a tsakanin wasu kabilu da makiya kuma, sai ya yi kira ga gwanatin tarayya da ta kafa kwamiti mai karfi a karkashin mai martaba Sarkin Zazzau, wanda ya na da tabbacin in har aka sa mai martaba Sarkin Zazzau a gaba, ire-iren wadannan matsaloli za su zama tarihi a cikin dan kankanin lokaci.

A karshen ganawar alhaji Ali Ba-Kware da wakilinmu, ya yi kira da sauran sarakuna da suke arewacin Nijeriya das u rika koyi da mai martaba Sarkin Zazzau na tabbatar da zaman lafiya a masarautunsu, kamar yadda sarkin Zazzau ya saw a gaba shekara 43 da suka gabata.

Exit mobile version