Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Rayuwar Sayyadina Abubakar Da Ayyukansa Na Yada Addinin Musulunci (IB)

by
3 years ago
in TARIHI
5 min read
Rayuwar Sayyadina Abubakar Da Ayyukansa Na Yada Addinin Musulunci (IB)
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Cigaba daga inda muka tsaya a makon jiya.

Ganin haka ta faru, ga gaskiya ta fito fili cewa akwai matsala wani ba Bakuraishe ba ya jibinci wannan lamari, kuma ga umarnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wanda shugaban nasu ya yi ikirari a kansa, sai jikinsu ya yi sanyi, ya kasance ba abinda ya rage a kansu sai mika wuya ga gaskiya. Don haka nan take Sayyadina Abubakar ya ce musu, to, in haka ne, ni na aminta ku nada dayan wadannan biyu dake tare da ni, Sayyadina Umar ko Abu Ubaidah domin ko wannensu ya cancanta.

Fadin haka da Sayyadina Abubakar ya yi sai wani daga cikin Ansaru ya ce, ni na samar mu ku da wata mafita mai sauki, ita ce, a nada shugabanni biyu, daya daga cikinku daya daga cikinmu. Sai Zaidu Dan Sabitu Radiyallahu Anhu (daya daga cikin Ansar din har wayau) ya ce, a’a, gaskiya dai ita ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne ya kasance shugaba, mu kuma mu ne mataimakansa. Don haka, a nada khalifa mu kuma mu taimaka masa. A nan ne Sayyadina Umar ya yi wata magana wadda ta dada kashe musu jiki baki daya. Ya ce, ya ku jama’a! Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama fa shi ne ya nada Abubakar don ya ba mu Sallah. A cikinmu wane ne yake iya mayar da shi baya shi ya shiga gaba?

Labarai Masu Nasaba

Tarihin Kafuwar Masarautar Nupe Da Jerin Sarakunanta

Tsarin Shugabancin Hausa/Fulani Gabanin Zuwan Bature

Da haka dai Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya nemi amincewar Sayyadina Abubakar don ya yi masa mubaya’a. Nan take kuma sauran jama’a gaba daya suka mara masa baya ba tare da wata jayayya da ta biyo bayan hakan ba. Washegari ranar Talata Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya zauna a kan mimbari sauran al’umma su kayi masa mubaya’a musamman Muhajirai da aka yi wancan taron ba da su ba.

Mubaya’ar Sayyadina Ali Gare Shi:

Ko Sayyadina Ali ya yi Mubaya’a Ga Sayyadina Abubakar? Manazarta sun kari junansu sani a kan wannan maganar. Abinda yake tabbatacce dai shi ne, Sayyadina Ali ya yi mubaya’a ga Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu amma ba a cikin gangamin farko da aka yi ranar Talata ba. To, ko akwai wani jinkiri mai yawa a tsakanin mubaya’arsa da ta sauran Sahabbai? Kuma mene ne dalilin hakan? Wannan shi ne muhallin da masana suke sabani a kansa.

Akwai dai wata muhimmiyar rana da Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya yi huduba wadda a cikinta yake cewa, Wallahi ban taba kwadayin sarauta ba a dare ko a safiya, ban kuma taba rokon Allah a kanta ba a sarari ko a boye. Bayan haka ne sai Sayyadina Ali da Zubairu suka tashi suka ba da hanzarinsu ga Sayyadina Abubakar, suna cewa, mu daman mun yarda da cancantarka ga wannan al’amari, domin mun san matsayinka a wajen Manzon Allah Sallallahu  Alaihi Wasallama, kuma mun san ya umurce ka da ka bada Sallah, amma mun ji zafin ba’a yi shawara da mu ba.

A ruwayar Abu Sa’id al Khudri, cewa ya yi, Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya duba a cikin mutane yana kan mimbari bai ga fuskar Sayyadina Ali ba, sai ya aika aka kiransa ya ce masa, ya aka yi kana kanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuma surukinsa sannan ka ke son ka raba kan Musulmai? Sai Sayyadina Ali ya ce masa, kada ka damu, ya mika hannunsa ya yi masa mubaya’a. (Al Bidaya Wan Nihaya na Dan Kasir (5/248 da 6/333) da Tarikh Dimashk na Dan Asakir (30/277)).

Daga cikin ra’ayoyin malamai kan fassara rashin gaggawar mubaya’arsa akwai masu alakanta shi da cewa, mai dakinsa wato Sayyadatul Nisa’il Alamina Nana Fadimah Alaihah Salatu Wasallama ta nemi a raba gadon Mahaifinta domin a ba ta nata kason. Sai Sayyadina Abubakar ya sanar da ita abinda ya ji daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa su Annabawa ba a gadon su, abin da duk suka bari ya zama sadaka ga Musulmai. Sai ita kuwa tace, Mahaifinta bai taba fada mata wannan maganar ba, domin kuwa ita ce ta karshen wanda tayi Magana da shi a Iyalansa. Saboda wannan ne Nana Fadimah Alaihah Salatu Wasallama ta yi fushi bata sake masa magana ba har ta koma ga mahalincinta. (A duba labarin neman gadonta a Fathul Bari (7/564) da sharhin Imam Nawawi a kan Sahihu Muslim (12/77)).

Akan wannan tsabanin ne, Shehin malami kuma garkuwar musulunci, maga yakin Ahlul Baiti, shugaban kungiyar hadin kan Al’ummar musulumai ta Africa, wato Sheikh Dr. Abduljabbar Kabara yake cewa, wannan tsabanin da yafaru tsakanin Sayyadina Abubakar da Nana Fadima ya kamata mu dauke shi a matsayin Mazhaba ce biyu, Mazhabar Nana Fadimah ana cin gadon Annabawa, mazhabar Sayyadina Abubakar kuwa ba’a cin gadon Annabawa. (cikin karatun littafinsa Mukaddimatul Azifa Juzu’I na biyu).

An ruwaito cewa Sayyadina Abubakar ya nemi izini wajen Sayyadina Ali akan ya nema masa izini a wajen Nana Fadimah domin yaje ya nemi afuwarta, kuma ta masa izini ya je ya roki afuwarta a kan fushin da take da shi, kuma ta yafe masa. (A duba Sunan Al Baihaki (6/301 da 471) da At Tamhid na Dan Abdul Barr, (8/164-180)).

A ra’ayin wasu malamai kuwa, wannan rashin jituwa a tsakanin Sayyadina Abubakar da uwar gidan Sayyadina Ali shi ya janyo jinkirin da Sayyadina Ali ya yi wajen ba da mubaya’arsa. To, amma ruwayar da mu ka ambata a baya tana nuna cewa damuwarsa a kan rashin shawartarsa ne a lokacin da aka nada Sayyadina Abubakar shi ya kawo jinkirin mubaya’arsa.

Duk yadda al’amarin ya kasance dai Sayyadina Ali ya yi mubaya’a ga Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu, ko a farko ko kuma daga baya. Kuma ya shiga cikin sha’anin gwamnatinsa, ya yi yaki a rundunonin da su kayi fada da wadanda su kayi ridda da wadanda suka soke rukunin Zakka. Kamar yadda ya ba da gudunmawa mai yawa wajen tafiyar da khalifancin Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ta hanyar shawarwarinsa masu amfani.

Jinkirin da ya yi kuma ba zai kawo gibi a sha’anin shugabanci ba, domin kamar yadda za mu gani a nan gaba, ba wani shugaban da bai gamu da irin wannan ba har Sayyidina Ali a lokacin nasa khalifancin.

Ayyukan Yada Addini:

Duk da karancin tsawon shekarun da ya yi a khalifanci, Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya yi ayyuka masu muhimmanci kuma masu yawan gaske wadanda suka yada manufofin Musulunci suka kafa daularsa, kana suka ba shi kariya daga sharrin makiya.

Tun farkon karbar aikinsa sai da ya shigar da duk sauran dukiyar da ya mallaka a cikin taskar gwamnati a matsayin sadaka zuwa ga Musulmai. Sannan ya ci gaba da sana’arsa kamar yadda ya saba. Daga bisani Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya lura da rashin yiwuwar hada aikin khalifa da kasuwanci, inda ya nemi Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya dakatar da kasuwancinsa a yanka masa albashi. A lokacin da ya bukaci karin albashi kuwa, sai da Sarkin Musulmai Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya nemi iznin jama’a a kan mimbari suka aminta illa wani mutumin kauye guda daya da ya ce su ba su aminta ba. Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya ce masa, ai ku mutanen karkara ‘yan amshi ne ga mutanen birni, in sun yarda ku sai dai ku ce Amin.

Za mu dakata a nan, sai wani makon mai zuwa idan Allah ya kai mu da rai da lafiya za mu cigaba. Kar ku manta ku na tare da dan ‘yar uwarku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri. 08098331260.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Sharhin Fim Din ‘Mijin Badariyya’

Next Post

Tausayi: Waye Bai Da Shi?

Labarai Masu Nasaba

Masarautar Nupe

Tarihin Kafuwar Masarautar Nupe Da Jerin Sarakunanta

by
8 months ago
0

...

Hausa/Fulani

Tsarin Shugabancin Hausa/Fulani Gabanin Zuwan Bature

by
9 months ago
0

...

Coomassie

Tarihin Tsohon Sifeta Janar Na ‘Yan Sanda Ibrahim Coomassie

by
10 months ago
0

...

Mai Martaba Aminu Ado Bayero: Sarkin Kano Na 15 A Daular Fulani

Mai Martaba Aminu Ado Bayero: Sarkin Kano Na 15 A Daular Fulani

by
11 months ago
0

...

Next Post

Tausayi: Waye Bai Da Shi?

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: