Rayuwar Sayyadina Ali Da Ayyukansa Na Yada Addinin Musulunci (V)

Da farko mu na mika sakon gaisuwarmu ga daukacin al’ummar Musulman da su ke biye da mu cikin wannan shiri na tarihin sahabban Annabi Sallalahu Alaihi Wasalam. Da fatan kowa ya na lafiya.

 

Cigaba daga inda mu ka tsaya a makon jiya.

 

Ba za mu yi mamakin Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya yi sha’awar Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya gaje shi ba, domin sun fi kama da juna a dabi’unsu da tsarin rayuwarsu kamar yadda Sayyadina Usman Radiyallahu Anhu ya fi kama da Sayyadina Abubakar a wajen sanyin halinsa da jin kunyarsa.

Da aka zabi Sayyadina Usman Radiyallahu Anhu, Sayadina Ali Alaihi Salatu Wasallam shi ne mutum na farko da ya yi masa mubaya’a kamar yadda ya tabbata a tarihi. Ya kasance a matsayin wazirinsa mai ba shi shawara ko da yaushe kamar yadda yake yi a zamanin Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu.

Nan gaba kuma za muji irin gudunmawar da Sayyidina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya bayar wajen kariya ga Sayyadina Usman Radiyallahu Anhu kafin Allah ya kaddara aukuwar abin da ya alkawarta na shahadarsa a hannun ‘yan tawaye.

 

Zaman Sayyadina Ali Khalifa na Hudu:

Bayan wafatin Sarkin Musulmai Sayyadina Usman dan Affan Radiyallahu Anhu, al’amurra duk sun rikice a birnin Madina. Ga shi kuma ba’a dawo daga aikin hajji ba, wanda Sahabbai da dama suna can, sai ‘yan tawaye suka fara tunanin hanyar da zata fisshe su. Abu na farko da sukayi tunani a kansa kuwa shi ne, su taka rawa wajen nada khalifa na gaba. A kan haka sun zagaya wurin Sayadina Ali Alaihi Salatu Wasallam da Dalhah da Zubairu da dan Umar Radiyallahu Anhuma, amma dukka sai suka yi biris da su, ko wanensu ya ki amincewa da ya karbi mubaya’arsu domin ba su ne ya kamata su yi wannan ba.

Haka dai al’amari ya dagule musu, suka rasa wanda zai fid da su daga wannan rami da suka auka, ga kuma alhazzai suna kan hanya sun kusa isowa Madina, sai suka yi barazanar kashe dukkan wadanda suka nema da wannan al’amari suka ki amincewa. Anan ne fa ya zama dole Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya karbi wannan aiki bisa ga shawarar wasu Sahabbai da suka lura al’amarin zai iya cabewa baki daya. An dai samu natsuwa kadan bayan yin mubaya’a ga Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam a Madina. Haka kuma bayan mutanen Madina daga Iraki ma (Biranen Kufa da Basrah) in da can ne mafi yawan ‘yan tawayen suka fito, an aiko da mubaya’a, haka ma mafi yawan sojojin Musulmai wadanda suke a wuraren yaki sun aiko mubaya’arsu.

Labarin kisan gilar da aka yiwa Sayyadina Usman Radiyallahu Anhu ta ci gaba da yaduwa a sauran birane, yana tafiya lokaci daya da labarin nada sabon Khalifa, shi ne Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam. Tambayar da mafi yawa suke fara yi ita ce, to, ina ‘yan tawayen? Me Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya yi game dasu da aka nada shi? Wace irin rawa ya taka yana Madina a lokacin faruwar wannan lamari? Rashin samun gamsasshiyar amsa ga wanda bai san hakikanin yadda abin ya faru ba, ta sanya mutane da dama daga sauran garuruwa kamar Misra da Yaman da Makka duk ba su yi mubaya’a ba.

Amma wadanda suka fi kowa adawa da wannan mubaya’a su ne mutanen Sham. Dalili kuwa shi ne, Sham tana karkashin rikon Mu’awiyah Dan Abu Sufyan wanda dan uwa ne na jini ga marigayi khalifa Sayyadina Usman Radiyallahu Anhu. Ga shi kuma nan take bayan faruwar wannan danyen aiki aka je da rigar Sayyidina Usman Radiyallahu Anhu wadda take cike da jininsa zuwa wurin Mu’awiyah a cikin yanayi wanda ke sa tausai da takaici a kan zaluntarsa da aka yi.

Mu’awiyah ya yi huduba mai gauni a kan wannan lamari, kuma ya nemi goyon bayan talakawansa a kan ramuwa da daukar fansa a kan ‘yan ta’adda. Mutanen Sham kuwa suka amsa kiransa kwansu da kwarkwatarsu. Har ma matan aure sai da suka dauki alwashi ba za su sake daukar janaba ba, sai an ga karshen ‘yan ta’adda.

Ikon Allah! Duk wannan abin da ke gudana shi Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam yana can Madina yana yanke shawarar sabunta gwamnati wadda kuma babu Mu’awiyah a cikinta, kamar yadda babu sauran mafi yawan gwamnoni wadanda ya gada daga gwamnatin da ta gabata. Da Allah ya so wannan lamarin zai kasance cikin sauki, da Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya dakata kamar yadda kaninsa Abdullahi Dan Abbas Radiyallahu Anhu ya nuna masa, ya bari sai mutanen Sham sun mika wiya, idan tafiya ta yi tafiya sannan sai ya canza Mu’awiyah. Amma hakan bata yuhu ba, domin kuwa ba haka Mabuwayin Sarki ya hukunta ba. Don haka sai Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya zartas da abinda ya yi niyya.

A Makka kuwa, Uwar Muminai Nana Aishah Radiyallahu Anhu tana can ba ta baro ba, domin ta nemi izinin Khalifa Sayyadina Usman Radiyallahu Anhu a kan zata yi aikin hajji, daga can ne kuma labarin kisan gilla da aka yi masa ya sameta. Tana cikin juyayin wannan lamari sai ga Dalha da Zubairu wadanda suka sulale daga Madina bayan sun yi wa Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam mubaya’a, sun nemi Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya bari su nemo goyon bayan jama’a daga sauran garuruwa don a gama da ‘yan ta’adda, amma Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallam ya ce, su dakata. Daga nan sai suka nuna masa suna da bukatar fita zuwa Makka amma bai san abin da su ke nufi ba. Shawarwari da tuntuba juna sun ci gaba a tsakanin jama’a a garin Makka bayan da ya tabbata cewa dai mafi yawan ‘yan tawayen har sun fice daga Madina sun nufi garuruwansu. Dalha da Zubairu sun ci nasarar shawo kan Uwar Muminai Nana Aishah Radiyallahu Anhu don ta fita tare da su ta karfafi jama’a akan babban jihadin da su ke son yi a kan ‘yan ta’adda. Kuma an yanke shawarar a nemo agaji daga Iraki, a kuma fara da ‘yan ta’adda dake can.

Da suka kama hanyar zuwa Iraki, kafin su je Basrah sun shuda da wani tafki wanda aka ambace shi da Al’Hau’ab. Jin an fadi sunansa ke da wuya sai Uwar Muminai Nana Aishah Radiyallahu Anha ta yi shirin komawa domin ta taba jin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yana ce wa matansa “Wacce ce a cikinku zata ji kukan karnukan Hau’ab, ta shiga gumuzun yaki har a kashe mutane a dama da hagunta, kuma ta tsira da kyar bayan ta kusa ta halaka?”

Al’amarin da Rabbus Samawati ya hukunta ba wurin kauce masa. Don haka sai Dalhah da Zubairu suka hana ta komawa, suka ce da ita, ba ruwanki da yaki, abin da muke so kawai shi ne, ‘ya’yanki Musulmai su gan ki, su san kina da goyon bayan wannan lamari don su samu kuzarin ba da himma a cikinsa. Uwar Muminia Nana Aisha Radiyallahu Anha sam bata gamsu da haka ba. (Al Awasim Minal Kawasim. Don tabbatar da ingancinta a duba Al Musnad na Imam Ahmad (6/52) da Al Mustadrak na Hakim (3/120) da Fathul Bari na Dan Hajar (13/45) da kuma Silsilatul Ahadis As Sahiha na Albani (1/473)).

 

Za mu dakata nan, sai mako mai zuwa zamu cigaba inda rai da lafiya.

Na sadaukar da wannan aikin nawa ga ruhin kanwata Fatima wacce Allah ya yi wa rasuwa a rana ita yau ta Litinin da ta gabata. Ina rokon Ubangiji Allah ya gafarta ma ta ya kai ladan gare ta. Amin.

Daga dan uwanku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri, 08098331260.

Exit mobile version