Mohammed Bala Garba" />

Rayuwar Sayyadina Umar Da Ayyukansa Na Yada Addinin Musulunci (B)

Cigaba daga in da muka tsaya a makon da ya gabata.

Wasu Darussa Daga Yake-yaken Zamanin Sayyadina Umar (R.A):

Da ya ke ba zai yiwu a irin wannan takaitaccen littafin nawa (Shiriya Ta Rahamanu) a fayyace labarin yake-yaken da su ka kai ga cin garuruwan da mu ka ambata a baya ba. Zai yi kyau mu bayyana kadan daga cikin darussan da a ke iya koyo daga cikinsu.

Darasi Na Daya: Hadin Kan Sahabbai A Yake-yaken:

Mu na iya cewa, dukkanin wadanda su ka cancanci zuwa yaki a wancan lokaci sun taka irin tasu rawa wajen samar da nasara ga yakin budar birane da Khalifa Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya shelanta.

An ba da labarin cewa, a yakin Kadisiyyah kawai sama da mutane saba’in daga cikin mayakan Badar su ka halarta. Fiye da mutane dari uku daga masu Bai’atur Ridhwan, fiye da dari uku daga jarumawan Fathu Makkah, fiye da mutane dari bakwai daga ‘ya’yan Sahabbai. Kai kusan ana iya cewa, ba wani kwararre ko gwani da bai fito da kwarewarsa ko ya bayyana bajintarsa ba a wannan yakin.

Darasi Na Biyu: Mayaka Sun Bayyana Jarumta Da Amana Da Imani:

Babu irin nau’in hakuri da jarunta wanda Musulmai ba su nuna ba a lokacin yake – yaken da mu ke magana a kansu. Misali a Farisa, Majusawa sun firgita da irin karfin halin Musulmai, wanda ya kai ga su ratsa kogin Dijla ba tare da jirage ba. Fitattun jarumawa irin Ka’aka’u Dan Amru da Nu’umanu Dan Mikrin sun ba da himma matuka a yakin Nahawand da Tustar.

A game da amana kuwa, Sarkin Musulmai da kansa sai da ya jinjina musu bisa ga irin tarin dukiyar da suka aiko da ita daga fagen fama zuwa fadarsa, ya na cewa, lalle wadanda suka kawo wannan dukiya amintattu ne. Sayyadina Ali ya ce masa, kai ne ka zamo amintacce don haka talakawanka suka bi sawunka. Daga cikin ganimomin da suka iso fadar Khalifa Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu kuwa, har da takobin Kisra (shugaban kasar Farisa) da na Hiraklu (shugaban Rum) da ababen ado da na more rayuwa iri-iri da kuma kayan alfahari na tarihi da suka mallaka wadanda kakanninsu ke bugun gaba da su.

Dangane da kishin addini kuwa, muna iya fahimtarsa daga labarin wani ladani mai kiran sallah wanda ya rasu a fagen fama, mutane duk su ka nuna sha’awarsu ga mukamin sa, sai da har aka kai ga yin kuri’a a tsakaninsu. (Tarikhul Umam Wal Muluk, na Dabari, (4/390)).

Wafatin Sarkin Muminai Sayyadina Umar Radiyallahu:

A karshen shekara ta Ashirin da uku bayan hijira ne Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya yi mafarkin wani jan zakara ya sakkwace shi sau biyu. Da ya labarta ma Asma’u diyar Umais Radiyallahu Anhu (matar da Sayyadina Ali ya aura bayan ta yi wa Sayyadina Abubakar takaba) wanda an san ta da fassarar mafarki, sai ta ce masa, wani ba’ajame zai kashe ka.

A tsarin gwamnatin Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu duk namijin da ya balaga daga cikin kafirai ba’a ba shi damar zuwa Madina. Amma Mughirah Dan Shu’ubah, gwamnansa na Kufa ya nemi izninsa domin ya turu masa wani yaro mai hazaka daga cikin ‘ya’yan farisa ana kiransa Abu Lu’lu’ata wanda kuma bai Musulunta ba. Yaron ya kware wajen sana’oin hannu kamar kira da sassaka da zane da makamantansu. Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya ba da izni.

Bayan da Abu Lu’lu’ata ya tare a Madina, ya nemi sassaucin harajin da Mughirah ya dora masa a wajen Sarkin Musulmai Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu. Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya tambaye shi nawa ka ke biya a shekara? Ya ce, Dirhami dari. Sayyadina Umar ya ce, mene ne sana’arka? Ya ce, kira da sassaka da zane. Sai Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya ce, to in haka ne ai Dirhami dari ba su yi ma yawa ba.

A daidai lokacin da Sarkin Musulmai ya ba da umurnin a rage ma Abu Lu’lu’ata haraji, shi kuma yana can yana shirin ganin bayansa.

A safiyar 26 ga watan Zull Hajji shekara ta 23 bayan hijira, Sarkin Musulmai Sayyadina Umar ya fito zuwa Masallaci kamar yadda ya saba, ba tare da dan rakiya ko wani jami’in tsaro ba. Da aka ta da Sallah Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya shiga gaba, ya daidaita sahun mutane sannan ya kabbarta. Gama Fatiharsa ke da wuya sai aka ji tsit, wadanda suke wajen Masallaci ba su san abin da ke gudana ba. Can kuma sai aka ji muryar Abdur Rahman Dan Aufu Radiyallahu Anhu yana ci gaba da Sallah, kuma ya takaita ta sosai.

Daga cikin Masallaci kuwa, wadanda ke kusa sun shedi Abu Lu’lu’ata ya kutsa a tsakanin mutane yana sukarsu da wuka, sai da ya soki mutane 13 kafin ya kai zuwa ga liman, ya kuma yi masa suka shida a wurare daban – daban, cikin har da wata guda daya a kuibinsa. Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu bai kai kasa ba sai da ya janyo Abdur Rahman Dan Aufu ya sanya shi a matsayinsa don ya ci gaba da ba da Sallah ga mutane. Bamajushe ya yi gaggawa don ya gudu, amma wani daga cikin mamu ya cire mayafinsa ya jefa masa. Da ya lura ba makawa za a kama shi sai ya soka ma kansa wukar a cikinsa nan take ya ce ga garinku.

Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya suma a kan zafin wuka da ta ratsa jikinsa. Ana gama sallah shi kuma yana farfadowa, sai ya tambaya, jama’a sun yi Sallah? Aka ce masa, eh. Ya ce, babu rabo a cikin Musulunci ga wanda bai yi Sallah ba. Ya umurci Abdullahi Dan Abbas Radiyallahu Anhu ya duba masa wane ne ya kashe shi, da ya ji cewa bamajushe ne, sai ya godewa Allah akan ba mai Sallah ba ne ya kashe shi. Sannan ya nemi ruwa domin ya yi alwala ya sake Sallah, amma sau uku duk lokacin da ya yi alwala sai zafin ciwo ya buge shi har ya suma, sai a na uku ya samu ya yi sallarsa ta karshe.

Da farko mutane ba su yi tsammanin Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu zai mutu ba, sai da wani likita ya zo ya hada wani magani ya ba shi ya sha. Da ya sha sai maganin ya fito ta inda aka soke shi a ciki. A nan ne likitan ya umarci Sarkin Musulmai da ya yi wasiyyah. Mutane sun soma kuka a kan jin cewa, za su yi rashin Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu, amma Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya hana ayi masa kuka yana mai kafa hujja da hadisin da ya ji daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, ana azabtar da matacce da kukan rayayyu a kansa.

Sahabbai sun kewaye Sarkin Musulmai Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu suna taya shi murnar samun shahada, suna tuna irin kyawawan abubuwan da ya gudanar a rayuwarsa, da ayyukansa a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma adalcinsa a cikin mulkinsa tare da yaba masa, da kuma yi masa fatar alheri. Amma duk a cikinsu babu wanda maganarsa ta yi wa Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu dadi kamar Abdullahi Dan Abbas, wanda bayan da ya kare jawabinsa Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya tambaye shi, za ka shede ni da wannan a gaban Allah? Nan take Sayyadina Ali Dan Abu Dalib ya ce ma Abdullahi Dan Abbas Radiyallahu Anhu, amsa masa ni ma ina tare da kai. Amma dai shi Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu kamar yadda yake cewa, fatar da nake in tsira da ladar jihadina tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, wannan aikin naku kuwa in na ta shi ba lada ba zunubi to, ba kome. (Siffarsu ta zo a cikin AlKur’ani. Duba Suratul Mu’minun aya ta 60).

Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya umurci dansa Abdullahi ya duba yawan bashin da ake bin sa, sai ya gaya masa cewa, bashin ya kai Dirhami dubu tamanin da shida (Dirhami. 86,000). Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya ce, ka tattara abin da mu ka mallaka ka biya bashin, idan bai isa ba ka nemi danginmu Banu Adiyyin su taimaka, idan sun kasa ka nemi Kuraishawa kar ka wuce su.

Sannan ya umurce shi da ya nemo masa izinin Uwar Muminai Nana Aishah Radiyallahu Anhu don yana son a rufe shi a cikin dakinta kusa da aminnansa guda biyu, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Sayyadina Abubakar Siddik Radiyallahu Anhu. Uwar Muminai Nana Aishah Radiyallahu Anhu ta tausaya ma Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ta ce, na aminta na bar masa hakkina, amma a da wurina ke nan da na so a rufe ni tare da mahaifina da mijina. Da Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya ji wannan bayani sai ya ce da dansa, ka sake neman izini idan aka dauko gawata za a shigar. Domin watakila ta ji kunyar rayuwata ne, idan ta sauya ra’ayinta kar a damu, a kai ni makabartar sauran Musulmai, ba komai.

A na haka ne wani saurayi ya shigo domin ya jajanta ma Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya ba shi hakuri, ya kuma yi masa addu’a kamar yadda sauran Musulmai su ke yi. Da ya ba da baya sai Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya lura da suturarsa ta zarce haddin Shari’ah, Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya sa aka kira shi ya yi masa nasiha yana mai cewa, ka daga zaninka don ya fi tsafta kuma ya fi daidai da yardar Allah.

Allahu Akbar! Haka dai zafin ciwo bai hana Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu yin aikin da ya saba na wa’azi ba. Kuma zai gama mulkin duniyar Musulunci bayan shekaru 12 amma ana bin sa bashin Dirhami 86,000.

Da yamma ta yi, Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya lura da kusantowar ajalinsa, sai ya umurci dansa da ya saukar da kansa daga cinyarsa ya ajiye shi a kan kasa don ya yi tawali’u ga Madaukakin Sarki. Ya ci gaba da furta kalmomi na neman gafarar Allah har mala’ikan mutuwa ya karbi rayuwarsa.

Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu bai bar duniya ba sai da ya shata ma Musulmai yadda za su zabi wanda zai gaje shi, ya kuma bar wasicci mai tsawo ga duk wanda aka zaba. Zamu kawo wasiccin akan khalifa na uku in Allah ya so ya yarda a mako mai zuwa.

Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya shugabanci Musulmai tsawon shekaru goma da wata biyar da kwana ashirin da daya.

A nan mu ka kawo karshen tarihin rayuwan Sayyadina Umar da ayyukansa na yada addininmu Musulunci, da fatan al’umma sun amfana da wannan tarihi sun dauki darussa ciki.

Mu kasance tare a mako mai zuwa cikin wannan jaridar mai albarka ta Leadership Ayau don jin tarihin khalifa na uku, wato tarihin rayuwan Sayyadina Usman da ayyukansa na yada addinin Musulunci.

Ni ne dalibinku, dan ‘yar uwanku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri. 08098331260.

Exit mobile version