Rayuwata Na Cikin Haɗari -Kansila Gloria

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Kansila da ke wakiltar mazaɓar Ngbebongun da ke ƙaramar hukumar Lamude a jihar Adamawa Honarabul Gloria Markson, ta zargi shugaban ƙaramar hukumar Mista Ɓrati Nzonzo da cewa ya jefa rayuwarta na cikin haɗari.

Misis Gloria wacce itace mataimakiyar shugaban majalisar kansilolin kuma sakatariyar kwamitin binciken kuɗaɗen shigar ƙaramar hukumar, ta na magana ne a wani taron manema labarai a Yola.

Yace tun da farko kwamitin ya nemi shugaban ƙaramar hukumar da ya bayanan wasu kuɗaɗen harajin da’ake karɓa, amma yaƙi daga nan sai aka tsigeta a matsayin mataimakiyar shugaban majalisar kansilolin, ta ce zasu sauƙeta daga sakataren kwamitin kuɗin.

“ni ce kaɗai mace atsakaninsu, amma sun tsigeni a matsayar mataimakiyar shugaban majalisar kansiloli, kuma sun shirya cire ne daga sakataren kwamitin binciken kuɗi, wannan ba ƙarfafawa bane ga siyasar mata.

“Ana buƙatar ganin mata sun shigo harkokin siyasa amma ba kowace mace zata Iya siyasa irin wannan da tursasawa haka ba.

“ amma ni tunda nayi alƙawari kuma na ɗau rantsuwa cewa zan wakilci mutane na kuma zan tsaya musu akan gaskiya, ba zai amince ba, kuma na ce  sai na kai wannan rahoton, shi yasa aka tunɓukeni amma ba laifi na yi ba.

“da yake sunsan nine na san komai a kan rahoon yasa suke mini barazar zasu illata min rayuwa kuma ni kaɗaice mace shi yasa suke neman su tsorata ni na kawo mu su rahoton kaga sun cimma burinsu.

“to abin da ya kawoni ina son in sanarwa kwamishinan ‘yan sanda da shugaban tsaron farin kaya DSS su san cewa gashinan suna yiwa rayuwa na barazana, suna ƙirana da wasu lambobin da ban sani ba suna cewa sai sun naƙasa rayuwa na.

“shi yasa na fito ina faɗin kukana idan har zamuyi ƙarfafa mata a siyasa da irin wannan ba kowace mace ne zata iya haka ba, kuma ba wanda yafi ƙarfin doka” inji Gloria.

“ina son ya sani rayuwa ta da ta iyali na yana hanun Allah, yana hanun shugaban ƙaramar hukumar Lamurde, idan wani abu ya faru dani shi za’a kama” injita.

Misis Gloria ta kuma buƙaci hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa EFCC da ta binciki yadda shugaban ƙaramar hukumar ke kashe kuɗaɗe a ƙaramar hukumar da cewa ba’a kashi kuɗin bisa tsarin da doka ta tanada.

To sai dai shugaban ƙaramar hukumar Lamurde Mista Ɓrati Nzonzo, yace shi ba zaice komai kan zargin da kansilar tayi mishi, yace maganar na gaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar.

 

Exit mobile version