Rayuwata A Shekara 90 Da Haihuwa — Shaikh Dahiru Bauchi

Hakika duk dattijon da aka ce ya haura shekara 90 a duniya yana da abin fada a kan tarihin rayuwarsa, domin irin su ne ake ce wa sun ga jiya kuma suna ganin yau sannan ana sa rai su ga gobe. A wannan makon, LEADERSHIP A Yau Juma’a ta kawo muku tsaraba daga daya daga cikin dattawa mafi abin mamaki a kasar nan, ta fuskar cewa duk da gashi sun tsufa tukuf amma har yanzu ana damawa da su. A wannan firar da wakilinmu Khalid Idris Doya ya yi da shehin malamin kuma jigo a Darikar Tijjaniyya, ya bayyana kusan komai na rayuwarsa ciki har da abincin da ya fi so. Sannan wane irin abinci ne ba ya ci a wannan shekarun nasa kuma yana da nasaba da yadda ake ganin yana da kwari a jiki har yanzu?. Har ila yau, ana masa lakabi da Bauchi a sunansa, sai dai kuma shi ba haifaffen Bauchi ba ne, to a ina aka haife shi? Wannan da sauran tambayoyi game da shi duk ya amsa.

Ga yadda hirar ta kasance:

Da farko, Akramakallah masu karatu za su so ka fara da tarihin rayuwarka…

Assalamu Alaikum Wa Rahammatullahi. Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukkanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu a rayuwa. ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiya biyu. To ni dukkanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne, a lokacin da Bauchi take hade da Gombe. Idan kuma aka raba Bauchi da Gombe, to mu Fulanin Bauchi ne, a lokaci guda kuma mu Fulanin Gombe ne. Ta wajen ubana ni Bafulatanin Bauchi ne, ta wajen uwata ni Bafulatanin kauyen Nafada ne da ke can Gombe. An haife ni ne a watan Junairu a shekarar 1927 wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 kalandar Musulunci, a ranar Laraba.

Sunan mahaifina Alhaji Usman dan Alhaji Adam wanda mahaddacin Alkur’ani ne. Ni na rayu ne a hanunsa inda na haddace Alkur’ani a hannunsa. Sunan mahaifiyata Hajiya Maryam. Daga baya ne aka tura ni duniya domin in je in gyara tilawata. Na shiga duniyar na kuma gyara tilawar tawa, lamarin da ya sanya wasu kan ce mini Gwani, wasu mutanen kuwa kira na suke yi da sunan Gangaran a fagen haddar Alkur’ani mai girma. A bisa haka ne ma mahaifina ya ce zai tura ni duniya in je in sake nemo ilimi, daga nan aka tura ni nan Bauchi domin neman ilimi. Na fara neman ilimi ban riga na samu ilimin da yawa ba, sai Allah ya sa Failar Shehu Ibrahim Kaulaha din nan ta bayyana. Daman shi baban nawa dan Tijjaniyya ne Mukaddami ne ta salsalar Umaru Futi, wato Muhammadu Ghali, muna cikin wannan gwagwarmaya ne shi kuma ya ba ni Darikar Tijjaniyya, a wajensa na haddace karatun Kur’ani kuma a wajensa na karbi Darikar Tijjaniyya shi Alhaji Usman din (mahaifisa kenan). Bayan da muka shiga Failar Shehu Ibrahim, sai ya zama kowace harka nawa sai ta hada da maganar Shehu Ibrahim. Alhamdu Lillahi na samu rabo mai tarin yawa a sha’aninsa, na soma yin tafsirin Alku’ani ne a wajajen 1950, sannan na yi aurena na farko a shekarar 1948. Cikin alherin da Allah Ya yi mini, ’ya’yana tun suna kanana suke haddace Kur’ani, da farko ‘ya’yana suna haddace Kur’ani tun suna ‘yan shekara 11, aka dawo 10, aka zo 9 har ya zamana cewa akwai ‘ya’yana da suka haddace Kur’ani suna ‘yan shekara bakwai-bakwai da haihuwa. Ina da ‘ya’yan da suka haddace Alkur’ani guda 53, kuma mutum biyu ne kawai basu raye daga cikinsu, wato Dakta Hadi da Ahmad, amma sauran duk suna raye yanzu haka.

 

Malam yana da ‘ya’ya da yawa, ta fuskar jikoki fa?

Alhamudu Lillahi, suna da dama (dariya sosai). Ina da jikoki mahaddata guda 43, amma ga baki dayansu sun kai dari da wani abu.

 

Ka fi fice da sunan Bauchi, mece ce silar da ta sa ba a haife ka a can ba?

Ka san mu Fulani dan fari a gidan uwarsa ake haifansa, sabili da haka ni an haife ni ne a garin Nafada garin mahaifiyata kenan, a nan Nafada aka haife ni.

 

Allah shi gafarta Malam, matanka nawa ne?

Matana hudu ne na kuma dade ina tare da mata hudu din nan, wasunsu sukan tsufa sai su yi ritaya da kansu sai kuma na sake samun wadansu matan. Matana hudu ne a halin yanzu.

 

Yanzu idan aka dubi karatunka na addini, a wane bangare ka fi kwarewa?

Na farko bangaren da na fi kwarewa sosai a kai ita ce sana’ata, shi ne Alkur’ani. Daga nan kuma ta bangaren tafsiri, a nan malaman tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri in ji su. A cikin abubuwan da na fi kwarewa Kur’ani, tafsiri sai kuma bangaren Ma’arifa. Ma’anar Ma’arifa shi ne ilimin zuciya wanda ake kiransa ilimin tarbiyya, a nan ma masu irin ilimi kan ce ina da sani a fannin. Shehu Ibrahim ya ce lallai na san wannan bangaren. Sauran ilimomi ina tattabawa, su hadisi, lugga, li’irabi, tasrifi, fikihu duk ina tattabawa.

 

Masu sauraron tafsirinka suna ganin idan aka yi maka tambaya a lokacin da kake tafsiri ka fi bada amsa ta hanyar bada misali maimakon amsa kai-tsaye, mece ce hikimar hakan?

Wato shi buga misali wata runduna ce ta Allah mai shigar da ilimi cikin kawunan mutane, idan ka kawo amsar magana sai ka buga misalin da za ta hau kan mutane domin fahimtar da su. Shi buga misali yana jawo hankali a fahimci mene ne aka fada. Misali na da matukar muhimmaci wajen bada amsa.

 

Ko ka yi karatun boko, in ka yi a wane mataki ka tsaya?

(Dariya)…. Ai ko ABCD ban yi ba. Ni ban yi karatun boko ba, ko ABCD ban je na koya ba.

 

Ba ka yi karatun Boko ba, yaya ake gwawarmayar rayuwa ta zamanin yau?

Eh to, da yake muna tare da masu bokon, masu karatun na boko, wasu ‘ya’yanmu sun zama daktoci ba daya ba, ba biyu ba. Don haka suna dafawa wajen tafiyar da komai yadda ya dace. Muna da masu karatun boko sosai a cikin ‘ya’yana da almajiraina kuma muna tare da su, ta haka muke gwagwarmayar rayuwar yau din.

 

Mene ne ya fi ba ka sha’awa a rayuwarka?

Abin da ya fi ba ni sha’awa, irin yadda na maida Kur’ani sa’anata da kuma yadda na rungumi Darikar Tijjaniyar nan ta zama rayuwata, kuma da dukkanin wani mutumin da yake dangantuwa da son Annabi da son Allah ina sha’awar in sadu da shi.

 

A lokacin da ya zamana ba ka karatun Kur’ani kana hutawa, me kake yi?

Wai! A duk lokacin da nake hutu ina shagaltuwa ne da karanta Salatil Fatihi, da Tasbihi da kuma Istigfari da Salatin Annabi da sauran zikiri. Nakan shagulta da zikirori ne a lokacin da nake hutawa.

 

Wane abinci ne Malam ya fi sha’awa a rayuwarsa?

(Cikin matukar dariya)… Abincin Hausawa da Fulani su nake sha’awa, ina cin tuwon shinkafa, ina cin shinkafar ita kanta. To amma yanzu a halin da muke ciki na daina cin dawa da masara, na kuma daina cin tuwon masara da tuwon gero duk na daina cin su yanzu, kuma babu wani likitan da ya hana ni cin su hankalina ne kawai ya ki su. Ka ga yanzu dai ina cin tuwon shinkafa da ita shinkafar kanta. Masara, tuwon masara, dawa, tuwon gero duk na yi ritaya da cin su a halin yanzu ba na cin su bisa ra’ayin kaina.

 

Exit mobile version