Connect with us

WASANNI

Real Madrd Ta Dauki Sabon Koci

Published

on

A yammacin jiya Talata ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ayyana daukar sabon koci wanda zai jagoranci ‘yan wasanta a kakar wasa mai zuwa.

Sanarwar, wadda kungiyar ta wallafa a shafukanta na yanar gizo, ta ce, mai horas da kungiyar kwallon kafa ta kasar Spaniya, Julen Lopetegui shi ne zai maye gurbin Zinedine Zidane, wanda ya ajiye aikin koyar da Real kwanaki kadan bayan ya lashe kofin Zakarun Nahiyar Turai.

Wannan sanarwa ta zo a daidai lokacin da mafi yawan magoya bayan kungiyar suke kallo wasu kwaca-kwacai na kasashen ketare a matsayin wadanda za su maye gurbi Zidane.

Tun bayan ajiye aikin Zidane, kungiyar ta fara zawarcin tsohon mai horas da kungiyar kwallo kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, na Totteham, Mario Pochettino, da kuma tsohon dan wasanta wanda a yanzu yake rike da karamar kungiyar a matakin kananan yara, Guti H.

Julen, ya bayyana farin cikinsa kan wannan gagarumin aiki da Real ta bashi, inda ya ce, dama ce ya kara samu domin nuna bajintarsa a fagen horas da ‘yan wasa musamman a babbar kungiyar kamar Madrid.

Julen, wanda tsohon dan wasan Madrid ne, ya fara harkar koyarwa a shekarar 2003 a matsayin mataimaki a karamar kungiyar ‘yan wasan kasar Spaniya, sannan ya rike matasa ‘yan kasa da shekaru 17, 29, 20 da kuma 21 kafin daga bisani ya tsallake zuwa kungiyar kwallon kafa ta FC Porto
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: