Abba Ibrahim Wada" />

Real Madrid Na Kan Tattaunawa Da Alcantara Na Bayern Munchen

Real Madrid ta cimma yarjejeniya da d an wasan tsakiya na Bayern Munchen Thiago Alcántara a wani yunkuri na maye gurbin d an wasanta Mateo Kovacic da ya tafi aro Chelsea.

Thiago Alcántara dai dama rahotanni sun bayyana cewa yana son barin kungiyarsa ta kasar Jamus don fuskantar wani kalubalen, kasancewar ya shafe shekaru biyar a kungiyar.

Sabon mai horas da kungiyar Real Madrid Julen Lopetegui  na daga cikin masu ganin cewa matashin d an wasan mai shekaru 27 zai zamo babban d an wasa a nan gaba.

Yanzu kawai abinda ya rage shi ne sanar da farashin da aka cimma don biya ya taho kungiyar.

Sai daga bangaren kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ta bayyana cewa bata da niyyar siyar da d an wasan nata wanda ta siyo daga Barcelona shekaru niyar da suka gabata akan kud i fam miliyan 30.

 

Exit mobile version