Real Madrid Su Na Bata Lokacinsu Akan De Gea – Mourinho

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana cewa Real Madrid suna bata lokacinsu ne kawai akan mai tsaron ragar kungiyar tasa, David De Gea domin dan mai tsaron ragar bana siyarwa bane.

Mourinho ya bayyana hakane bayan kungiyarsa ta tashi daga wasan da suka buga da Sebilla inda yace ya kamata su nemi wani mai tsaron ragar saboda bazasu samu abinda suke so ba a Manchester United.

Yaci gaba da cewa idan shine shugaban gudanarwar kungiyar ta Real madrid da tuni ya hakura da neman De Gea saboda yana neman abinda bazai samu ba kuma yana bata lokacinsa domin idan ya hakura zai iya samun wani a wata kungiyar.

Real Madrid dai tana shirin yin garambawul a kungiyar bayan da kungiyar takasa abin azo agani a gasar laliga kuma tuni shugaban kungiyar ya shirya kashe kudi domin siyan duk dan wasan da yake so.

Dabid De Gea dai shine mai tsaron ragar da Real Madrid take zawarci sai kuma mai tsaron ragar kungiyar Chelsea, Thibaut Courtoise wanda kungiyar  shima take zawarci idan bata samu De Gea ba.

Sai dai Mourinho ya bayyana cewa mai tsaron ragar babu inda zashi a wannan kakar domin ya shirya cigaba da buga wasa dashi har zuwa kakar wasa mai zuwa.

Dabid De Gea dai yanada ragowar watanni 16 a ragowar kwantaragin daya rage masa a kungiyar.

Exit mobile version