Abba Ibrahim Wada" />

Real Madrid Ta Sake Komawa Neman Kante

Kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid ta shirya tsaf domin takara da Jubentus wajen kokarin sayo dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, N’golo Kante kamar yadda jaridu daga kasar Ingila suka rawaito.

Dan wasan na Faransa ya nuna kansa sosai musamman a lokacin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, sannan kuma ya na daya daga cikin zaratan ‘yan wasan tsakiya da a yanzu ake ji da su, abin da ya sa Real Madrid ta fara tunanin dauko shi.

Madrid na tantama kan Casemiro, tana ganin ba shi da karsashin ci gaba da rike mata tsakiya, shi ya sa ta fara hararo Kante yayinda kuma manyan ‘yan wasanta na tsakiya da suka hada da Toni Kroos da Luca Modric duka shekaru sun fara yi musu yawa.

Real Madrid a shirye take ta bayar da zunzurutun farashin fam milyan 70 domin sayo dan wasan mai shekaru 28 yayinda kungiyar kwallon kafa ta Jubentus ma ta shirya kashe kudi akan dan wasan tsakiyar wanda kawo yanzu yana daya daga cikin masu taimakawa Chelsea.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German tana cikin kungiyoyin da suke zawarcin Kante, wanda Chelsea ta sayoshi daga kungiyar Leceister City a lokacin tsohon kociyan kungiyar, Antonio Conte.

Sai dai abune mai wahala Chelsea ta ahkura ta sayar da dan wasan tsakiyar nata wanda take ganin idan ta sayar dashi bazata iya samun wanda zai maye mata gurbinsa ba inda tuni kungiyar ta shirya yin fatali da duk wani tayin kudin da za’a kawo mata.

Exit mobile version