Duk da cewa, kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi nasarar doke Balencia a wasan gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi kuma a wasan da Real Madrid ta doke Balancia da ci 2-0 ne dan wasa Dani Carbajal ya koma buga wa kungiyar wasa bayan jinya da ya yi mai tsawo. Sai dai minti 25 kacal ya buga daga baya aka cire shi aka saka Lucas Bazkuez ya canje shi a wasan na mako na 23 a gasar La Liga kuma rabonda da dan kwallon Spaniyan ya buga wa Real Madrid wasa tun ranar 2 ga watan Janairu a karawa da Celta Bigo, bayan da ya yi rauni saura minti biyar a karkare fafatawar.
Watakila Dani Carbajal ba zai yi wa Real Madrid gasar Champions League da za ta yi da Atalanta ba ranar 24 ga watan Fabrairu sai dai kawo yanzu jerin ‘yan wasan Real Madrid da ke jinya sun hada da Sergio Ramos da Eder Militao da Albaro Odriozola da Eden Hazard da Rodrygo da Fede Balberde da kuma Marcelo.
Me Ya Sa ’Yan Wasan Ke Tafiya Ciwo?
Real Madrid wadda take rike da gasar La Liga, ba ta kare kofinta na Spanish Super Cup ba a shekarar nan, an kuma yi waje da ita a gasar cin kofin Copa del Rey bayan karamar kungiyar Alcoyano tayi waje da ita.
Yanzu dai ta mayar da hankali ne kan lashe gasar La Liga wanda take ta uku a kan teburin wasannin bana da kuma gasar cin kofin zakarun turai na Champions League da za ta kara da kungiyar Atalanta a cikin watan nan na Fabrairu.
To sai dai da yawan ‘yan kwallon Real Madrid na fama da jinya da hakan zai iya zama barazana kan kokarin da take na ganin ta tsira da kofi a kakar nan duk da cewa kungiyar ba ta kokari musamman idan tana buga wasa da kana nan kungiyoyi.
A satin daya gabata likitoci suka yi wa kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos tiyata a kafarsa ya kuma bi sawun masu jinya da suka hada da dan wasa Eden Hazard da Rodrygo da Dani Carbajal da Marcelo da kuma matashin dan wasa Fede Balberde.
Sau 38 ‘yan wasan Real Madrid guda 20 suka yi rauni a kakar bana mai cike da kalubale sai dai daman Real Madrid ba ta dauki dan kwallo ba a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021, kuma cutar korona ta kawo tsaiko da ta kai ana buga wasanni da yawa a karamin lokaci.
Real Madrid wadda take ci gaba da fuskantar barazanar rashin nasara za ta fuskanci kalubale a watan Fabrairu, wadda za ta yi wasanni shida har da daya a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League a bana.
Real Madrid ta kai zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai, sai dai tana ta uku a teburin La Liga da maki 43 iri daya da wanda Barcelona keda shi ta biyu a teburi kuma Atletico Madrid ce ta daya mai kwantan wasa daya.
Saboda haka ya zama wajibi Real Madrid ta saka kwazo a watan na Fabrairu, idan ba haka ba ta fuskanci kakar bana ba tare da ta lashe kofi ba kuma Real Madrid za ta fafata da kungiyar Balladolid a wasan tan a gaba.
Sannan kwana uku tsakani Real Madrid za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Getafe a kwantan wasan tun na makon farko da basu buga ba sakamakon dage wasan da akayi saboda nisan da sukayi a gasar zakarun turai na kakar data gabata.
A dai makon wato ranar Lahadi Real Madrid za ta buga gasar La Liga a gida da kungiyar Balencia a filin ta na Di Stefano sannan daga nan ne Real Madrid za ta ziyarci Real Balladolid a gasar La Liga ranar Lahadi 21 ga watan na Fabrairu.
Real Madrid za ta ziyarci kungiyar kwallon kafa ta Atalanta domin buga wasan farko a zagaye na biyu a gasar Champions League ranar Laraba 24 ga wata sannan kungiyar za ta karkare watan Fabrairu da gasar La Liga da za ta karbi bakuncin Real Sociedad.
Wasannin da Real Madrid za ta kara a Fabrairu:
Ranar Lahadi 21 ga watan Fabrairu La Liga
Balladolid bs Real Madrid
Ranar Laraba 24 ga watan Fabrairu Champions League
Atalanta bs Real Madrid
Ranar Lahadi 28 ga watan Fabrairu La Liga