Abba Ibrahim Wada" />

Real Madrid Ta Sayi Mendy

Kungiyar  kwallon  kafa ta Real Madrid ta amince da siyan dan wasan baya na  kungiyar  kwallon  kafa ta Lyon, Ferland Mendy, wanda tuni  kungiyoyin biyu suka amince da farashin dan wasan kuma kowanne lokaci daga yanzu Real madrid zata iya bayyana dan wasan a gaban magoya bayanta.

A jiya ne kuma Real Madrid ta tabbatar da siyan dan wasan gaba na  kungiyar  kwallon  kafa ta Eintract Frankfurt, Luca Jobic, bayan dan wasan ya rattaba hannu na tsawon shekaru shida da  kungiyar wadda take buga gasar Laliga bayan da tun farko kuma  kungiyar ta siyi dan wasan baya daga FC Porto, Elder Militao.

Bayan doguwar tattaunawa tsakanin Real Madrid da dan wasan kawo yanzu dai ya amince zai saka hannu na tsawon shekaru shida  a Real Madrid inda zai maye mata gurbin dan wasa Marcelo wanda zai bar  kungiyar a kakar wasa ta gaba.

Wasu rahotanni kuma sun bayyana cewa dan wasa Sergio Reguilon da Theo Harnandez suma zasu bar  kungiyar idan har aka tabbatar da siyan Mendy wanda  a yanzu haka yake wakiltar  kasar Faransa a wasannin  kasashen da take bugawa.

Har ila yau ana cigaba da tattaunawa tsakin Real Madrid da Chelsea akan dan wasa Edin Hazard wanda  kungiyar ta sa tace dole sai Real Madris ta  kara kudi idan har tana son a cigaba da cinikin wanda akayi tsammanin zai kai fam miliyan 106.

Kociyan  kungiyar  kwallon  kafa ta Real Madrid dai yayi al kawarin siyan ‘yan wasa da yawa domin  kara  karfi bayan da  kungiyar tasha kashi a wasanni da dama a kakar wasan data gabata inda tayi ta uku a laliga.

Exit mobile version