Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Real Madrid Ta Sayi Wanda Ake Wa Lakabi Da “Messin” Japan

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tabbatar da sayen dan kasar Japan Takefusa Kubo ranar Juma’a, dan wasan mai shekaru 18 ya koma Real Madrid daga kungiyar kwallon kafa ta FC Tokyo kuma zai taka leda a tawagar Madrid B, watau Castilla, a kakar wasa mai zuwa, Takefusa Kubo zai koma Castilla a kakar wasa ta gaba,’ in ji wani bayani na Real Madrid. Dan wasan tsakiyan ya kasance daya daga cikin shahararrun yaran ‘yan wasan kwallon kafa na duniya masu fasaha.’

Kubo, wanda aka mishi shi lakabi da “Messin Japan”, ya bugawa kasar sa wasan farko a wannan watan a wasan da suka buga da El Salvador. Kungiyoyin kwallon kafa irin su Barcelona, Paris Saint-Germain da kuma Manchester City na daga cikin kungiyoyin dake zawarcin dan wasan, Kubo ya samu lakabin da ake masa lokacin da yake Barcalona Academy sannan yana da shekaru 10 da haihuwa, amma ya koma Japan a 2015 saboda sakamakon takunkumi da FIFA ta sawa kungiyar sakamakon saba wa dokar siyan yan wasa masu karancin shekarun haihuwa.

Kubo ya shigo a matsayin canji bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a wasan da Japan ta ci El Salvador biyu da nema a karshen makon da ya gabata, kuma an sanya shi a cikin jerin yan wasan da zasu wa kasar Japan gasar Copa America wanda ya fara ranar Juma’a a Brazil, Kubo ya zira Tokyo kwallaye hudu a wasanni 13 da ta buga a gasar J-League a wannan shekarar. Japan ta bude gasar cin kofin Copa America karo na biyu da Chile a Sao Paulo ranar Litinin

Exit mobile version