Damar da Real Madrid keda ita na kai wa zagaye na biyu a Gasar cin kofin zakarun turai na Champions League na reto, bayan da kungiyar kwallon kafa ta Shakhtar Donetsk daga kasar Ukraine ta doke ta daci 2-0.
Real Madrid ta je Ukraine ne a wasa na biyar-biyar a cikin rukuni na biyu a gasar ta zakarun Turai ta shekarar nan ranar Talata kuma a minti na 45 na farko da suka fafata sun je hutu babu ci, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Shakhtar ta ci kwallye biyun ta hannun dan wasa Bruno Ferreira Bonfim wanda yaci kwallon farko sannan Manor Solomon ya kara ta biyu.
A wasan farko da kungiyoyin biyu suka kara a cikin watan Oktoba, Shakhtar ce ta yi nasara da ci 3-2 a Spaniya sannan da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta uku da maki bakwai, ya yin da Shakhtar ta karbe mataki na biyu itama da makinta bakwai a rukuni na biyun.
Ranar 9 ga Disamba za a karkare karawar cikin rukuni, inda Real Madrid za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Borussia Munchengladbach a Spaniya bayan da a wasan farko kungiyoyin suka buga 2-2 a kasar Jamus.