Abba Ibrahim Wada" />

Real Madrid Ta Siya Ferland Mendy Daga Lyon

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kammala siyan dan wasan baya na bangaren hagu, Ferland Mendy daga kungiyar kwallon kafa ta Lyon akan kudi fam miliyan 48.

Dan wasan ya ja hankalin kociyan Real Madrid, Zinadine Zidane sakamakon kokarin da yayi a kakar wasan data gabata inda ya buga wasanni da dama a kungiyarsa ta Lyon kuma kociyan tawagar kasar Faransa ya gayyaceshi a wasannin da kasar ta buga a satin daya gabata.

A ranar Laraba, 19 ga watan Yuli Real Madrid zata gabatar da dan wasan a gaban magoya bayanta a filin wasa na Santiago Bernabeu.

Kawo yanzu Mendy ne dan wasa na uku da kungiyar ta siya a wannan kakar bayan da kungiyar ta siyi dan wasa Luca Jobic daga Frankfurt da Edin Hazard daga Chelsea kuma kungiyar tana cigaba da Neman Dan wasan Manchester United, Paul Pogba da kuma Cristian Eriksen daga Tottenham ta kasar Ingila.

Exit mobile version