Abba Ibrahim Wada" />

Real Madrid Ta Ware Fam Miliyan 300 Kan Neymar

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ware makudan kudade har fam miliyan 300 domin tun karar kungiyar kwallon kafa ta PSG akan ko zata siyar mata da dan wasanta na gaba Neymar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Neymar dai yakoma PSG daga Barcelona a shekara ta 2017 inda ya zura kwallaye 48 cikin wasanni 53 daya bugawa kungiyar kuma ya taimaka mata ta lashe gasar cin kofin rukuni rukuni ta kasar Faransa.
Tun bayan daya koma PSG akan kudi fam miliyan 200 ake ta hasashen cewa zai sake komawa kasar Sipaniya domin bugawa Real Madrid wasa ko kuma yakoma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona wadda ya bugawa wasa tsakanin shekarun 2013 zuwa 2017 kuma ya zura kwallaye 100 cikin wasannin daya bugawa kungiyar.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tayi shirin siyan babban dan wasa a wannan kakar mai zuwa bayan da a kakar wasan data wuce ta siyar da Cristiano Ronaldo amma kuma bata mayar da gurbinsa ba.
Dan wasan Chelsea, Edin Hazard, shine wanda Real Madrid tayi niyar siya sai dai kawo yanzu ana ganin kungiyar zata canja akalar neman Hazard din da neman Neymar, wanda zata kashe kudi kafin ta sameshi.
Sai dai ana ganin abune mai wahala dan wasa Neymar, wanda a yanzu haka yake jiyya yakoma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona duba da yadda ake adawa tsakanin tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona da Real Madrid.

Exit mobile version