Abba Ibrahim Wada" />

Real Madrid Ta Ware Fam Miliyan 85 Domin Sayan N’Golo Kante

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ware kudin daya kai fam miliyan 85 domin sayan dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta cheslea, N’Golo Kante, wanda ya lashe kofin firimiya da Chelsea a kakar wasansa ta farko a lokacin tsohon kociyan kungiyar, Antonio Conte.
Dan wasan ya buga wasanni 150 a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tun bayan komawarsa daga kungiyar Leceister City a kakar wasa ta 2016 zuwa 2017 kuma yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka taimakawa Leceister City ta lashe firimiya a shekara ta 2016.
A farkon shekara ta 2018 ne dan wasan dan kasar Faransa ya sake sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta Chelsea wadda zata kai shi har kakar wasa ta shekara ta 2023 sai dai komai zai iya canjawa nan gaba kadan.
Tun farkon fara wannan kakar dai aka fara rade radin cewa Kante zai iya barin kungiyar tasa sai dai kociyan na Chelsea, Frank Lampard ya karyata jita-jitar inda yace dan wasan babu inda zashi kuma yana farin ciki a kungiyar ta birnin Landan.
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane ne ya nuna cewa yana son kungiyarsa ta sayo masa Kante mai shekara 28 a duniya sai dai abune mai wahala Lampard ya amince ya rabu da shahararren dan wasan tsakiyar tasa.
Har ila yau wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafan dai ta Real Madrid ta shirya bawa Manchester United fam miliyan 72 tare da hada mata da wasu daga cikin ‘yan wasanta guda biyu da suka hada da James Rodriguez da Mariano Diaz domin sayan Paul Pogba.

Exit mobile version