Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, wadda kuma itace take riƙe da kofin La Liga na ƙasar Spaniya, Real Madrid ta yi rashin nasara a karon farko a hannun a Girona da ci 2-1 a wasan mako na 10 da suka kara a ranar Lahadi.
Real Madrid ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Isco a minti na 12 da fara wasan, kuma haka aka je hutun rabin lokaci tana kan gaba da ƙwallo daya.
Bayan da aka dawo ne Girona ta farke ƙwallo ta hannun Cristhian Stuani daga baya kuma Portu ya ƙara ƙwallo ta biyu.
Wannan ne karo na biyu da aka ci Real Madrid a La Liga, bayan da ta yi rashin nasara da ci daya mai ban haushi a hannun Real Betis a Barnebeu a ranar 20 ga watan Satumbar daya gabata
Real Madrid ɗin dai tana fama da masu zura ƙwallo a raga sakamakon rashin zura ƙwallaye da yan wasa Ronaldo da Benzema suke fama dashi.
Real Madrid dai za ta fafata wasanta nag aba a gasar zakarun turai da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham ta ƙasar ingila a ranar Laraba a filin wasa na Wembley dake birnin landan.