Real Madrid Tana Da Karfin Sayan Haaland Da Mbappe, Cewar Shugaban Laliga

Madrid

Shugaban hukumar da ke kula da gasar Laligar na kasar Sifaniya, Javier Tebas ya yi ikirarin cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tana da isassun kudaden da za ta iya sayen Kylian Mbappe da Erling Haaland a shekara mai zuwa.

Tebas ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce ba kamar shekarar da ta gabata ba, a halin yanzu Real Madrid ta samu kudade da za ta iya sayan wadannan manyan ‘yan wasa.

Real Madrid din dai ta gaza a kokarin da ta yi na sayen Mbappe daga Paris Saint Germain a watan da ya gabata, domin har sai da kungiyar ta Laliga  ta ta yi tayin bada fam miliyan 137, amma PSG ta yi fatali da wannan tayi.

Real Madrid ta kara kudin zuwa fam miliyan 145 har da wasu jerin kari da suka kai fam miliyan 9 jimilla, amma duk da haka kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta ce ba ta san wannan zance ba.

A ranar karshe ta kasuwar hada-hadar ‘yan wasa, Real Madrid ta kara tayin bai wa PSG fam miliyan 189 a kan matashin dawasa Mbappe, amma sai ta ji shuru daga kungiyar ta kasar Faransa.

Exit mobile version