Real Madrid Tana Zawarcin Neymar Da Lewansowski Da Hazard

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi imanin cewa lokaci ya yi ta sayi dan wasan PSG, Neymar, da dan wasan Chelsea, Hazard da kuma dan wasan Bayern Munich Robert Lewandowski.

Neymar ya koma kungiyar PSG ne a cikin watan Agustan shekarar data gabata a kan kudi fam miliyan 200 wanda hakan ya sa dan wasan a yanzu ya fi kowanne dan wasa tsada a duniya.

Shi ma dan wasa Edin Hazard ya ki amincewa da sabon kwantaragin da kungiyar ta sa ta Chelsea ta yi masa tayi inda a kwanakin baya mahaifin dan wasan ya ce dan wasan ba zai sake sabuwar yarjejeniya da kungiyar ba.

Real Madrid ta dade tana zawarcin dan wasan gaba na Bayern Munchen, Robert Lewandowski, dan asalin kasar Poland wanda ya koma Munich din daga kungiyar Borussia Dortmund.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tana neman manyan ‘yan wasa a daidai wannan lokaci domin ci gaba da tunkarar Barcelona wadda take kan ganiyar siyan manyan ‘yan wasa a halin yanzu.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ta Real Madrid za ta iya samun Hazard ne kawai sannan watakila da Lewandowski amma Neymar abu ne mai wahala ya koma kasar sipaniya da buga wasa a ‘yan shekarun nan.

 

 

Exit mobile version