Real Madrid Za Ta Buga Wasan Sada Zumunta Da Rangers

Rangers

Tawagar Real Madrid za ta ziyarci birnin Glasgow, domin buga wasan sada zumunta da kungiyar kwallon kafa ta Rangers ranar 25 ga watan Yuli kuma shi ne wasan farko da Carlo Ancelotti zai ja ragamar Real Madrid a karo na biyu da zai horar da kungiyar.

Real Madrid din za ta kara da Rangers wadda ta lashe kofin gasar Scotland a kakar da ta kare tare, wadda tsohon dan wasan Liberpool, Steben Gerrard ke koyarwa kuma Real Madrid za ta buga wasannin sada zumunta biyu ko uku, domin shirin tunkarar kakar bana ta 2021 zuwa 2022, wadda za ta fara karawar farko da Alabes a La Liga ranar 14 ga watan Agusta.

Wasan karshe da kungiyoyin suka kara shine wanda Real Madrid ta doke Rangers 7-0 a European Cup sai dai Gerrard zai ja ragamar kungiyar wasan cike gurbin shiga gasar Champions, sakamakon da Rangers ta lashe kofin gasar Scotland a kakar da aka karkare.

Tuni dai Real Madrid ta koma filin daukar horo tare da ragowar ‘yan wasanta da a yanzu hala suka koma sai dai akwai wadanda basu koma ba har yanzu sakamakon buga wasannin nahiyar turai da gasar Coppa America da a yanzu ake fafatawa shima.

Exit mobile version