Abba Ibrahim Wada" />

Real Madrid Za Ta Iya Sake Lashe Kofin Zakarun Turai

Zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zata iya lashe kofin zakarun turai na wannan shekarar duk da cewa kungiyar tana fama da matsaloli kamar yadda tsohon dan wasan kungiyar, Clerance Seedorf ya bayyana.
Real Madrid ce dai ta lashe kofin sau uku a jere ciki har da wanda ta doke kungiyar Liverpool daci 3-1 a kakar wasan data gabata a wasan da aka buga a kasar Ukraine sai dai tsohon dan wasan ya ce duk da hakin da kungiyar take ciki zata iya lashe kofin.
Acikin kwanaki hudu Real Madrid tayi rashin nasara a hannun Barcelona har sau biyu yayinda wasan farko Barcelonan ta fitan da Madrid din daga gasar cin kofin Copa Del Rey yayinda daga bisani kuma bayan kwana hudu a gasar laliga Barcelona ta sake samun nasara daci 1-0 a filin wasa na Santiago Barnabue.
“Shekarar data gabata ma sunsha wahala sosai amma kuma a karshe suka je suka lashe kofin zakarun turai saboda haka Real Madrid zasu iya yin komai musamman a gasar kofin nahiyar turai” in ji Seedorf
Yaci gaba da cewa “Matasan ‘yan wasan kungiyar suna kokari amma kuma matashin dan kwallo bazai samu gogewa ba idan babu manyan ‘yan kwallo wadanda zai koya daga wajensu saboda haka dole sai kungiyar ta rike wasu daga cikin tsofaffin ‘yan wasanta”
Seedord, dan asalin kasar Holland wanda ya bugawa Real Madrid wasa a shekarun baya ya lashe gasar cin kofin zakarun turai da kungiyar kafin daga baya kuma yakoma kungiyar kwallon kafa ta AC Millan inda anan ma tauraruwarsa ta haska sosai.

Exit mobile version