Abba Ibrahim Wada" />

Real Madrid Za Ta Nemi Erickson Idan Modric Ya Tafi

Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta nemi d an wasan Tottenham, Cristian Erickson domin maye gurbin Luca Modric wanda yakeson barin kungiyar.

Luca Modric dai ya bayyana wa shugabannin kungiyar ta Real Madrid cewa yanada burin barin kungiyar domin komawa kungiyar Inter Millan ta kasar Italiya bayan da kungiyar ta bayyana cewa tana bukatarsa.

Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tafara tunanin buga wasa babu Modric ta hanyar fara neman wanda take ganin zai mata gurbinsa idan yatafi bayan ya shafe shekaru shida a kungiyar.

Sai dai tuni kungiyar kwallon kafa ta Tottenham tafara tattaunawa da d an wasan domin sake sabon kwantaragin a kungiyar bayan da kungiyar taga kungiyoyi irinsu Barcelona da Real Madrid da PSG sun fara zawarcinsa.

A kwanakin baya dai d an wasa Modric ya bayyana Erickson a matsayin babban d an wasa kafin had uwar kasar Denmark da Croatia a gasar cin kofin duniyar da aka kammala a kasar Rasha a watan da ya gabata.

Sai dai Real Madrid tana tsoron tuntubar kungiyar kwallon kafa ta Tottenham akan d an wasan bayan da aka bayyana shugaban kungiyar ta Tottenham a matsayin mutum mai wahalar sha’ani musamman idan za’a siyi d an wasansa.

Exit mobile version