Connect with us

WASANNI

Real Madrid Za Ta Nemi Pogba A Kaka Mai Zuwa

Published

on

Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zata tuntubi Manchester United ko zata iya siyar mata da dan wasanta Paul Pogba domin yakoma kungiyar a kakar wasa mai zuwa.
Pogba, wanda yakoma Manchester United daga kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dake kasar Italiya rahotanni sun bayyana cewa bayajin dadin zama a kungiyar sakamakon canjin wajen buga wasa da mai koyar da yan wasan kungiyar, Jose Mourinho yayi masa sannan kuma kungiyar bata samun nasara a wasu wasannin.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ware zunzurutun kudi sama da fam miliyan 500 a kakar wasa mai zuwa domin yin garambawul a kungiyar sakamakon rashin buga abin azo agani da kungiyar tayi a kakar data gabata kuma har yanzu bata maye gurbin Ronaldo ba.
Tuni aka bayyana cewa Pogba yana daya daga cikin yan wasan da kungiyar zata nema domin kara karfin kungiyar sai dai dole zata fuskanci kalubale kafin Manchester United ta amince da siyar da dan wasan wanda yafi kowanne dan wasa tsada a kungiyar a lokacin data siyeshi fam miliyan 83 daga Jubentus din Italiya.
Sannan Real Madrid tana bukatar ta ware kudi kusan fam miliyan 150 domin siyan dan wasan wanda yabuga wasanni 74 sunnan ya zura kwallaye 19 tun daga lokacin da yakoma Manchester United din.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: