Abba Ibrahim Wada" />

Real Madrid Za Ta Yi Zawarcin Dan Wasan Bayern Munchen Gnabry

Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta saka sunan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, Serge Gnabry a cikin ‘yan wasan da zata nema a kakar wasa mai zuwa kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Dan wasan dai ya zura kwallaye hudu rigis a wasan da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen tayi fata-fata da kungiyar Tottenham har gida daci 7-2 a gasar cin kofin zakarun turai wanda hakan yasa ya zura kwallaye biyar sannan ya taimaka aka zura guda hudu cikin wasanni takwas daya buga  a wannan kakar.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana kokarin da dan wasan yayi shine yaja hankalin shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid suka saka shi acikin jerin sunayen ‘yan wasan da zasu nema a karshen wannan kakar.

Gnabry dai tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ne sai dai tauraruwarsa bata haskawa ba tsawon zamansa a kungiyar wanda hakan yasa ya koma kungiyar Werder Bremen ta kasar Jamus kuma a kakar wasa ta 2016 zuwa 2017 kokarinsa yasa kungiyar Bayern Munchen taga yakamata ta daukeshi.

Har ila yau dan wasa Gnabry yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan da tawagar ‘yan wasan kasar Jamus take ji dasu inda ya zura kwallo tara cikin wasanni goma cikin wasannin da kociyan tawagar Joachim Low ya gayyacishi.

Sai dai abune mai wahala kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ta hakura ta rabu da matashin dan wasan wanda take ganin shine zai kasance jagoran kungiyar a nan gaba saboda har yanzu shekararsa 24 a duniya.

Exit mobile version