Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja
Kasar Birtaniya ta dora alhakin cigaba da watsa labarai da gidan rediyon Biyafara ke yi a Ingila kan gwamnatin tarayyar Nijeriya. Wannan martani ya biyo bayan zargin da ministan yada labaran Nijeriya, Mista Lai Mohammed, ya yiwa kasar ta Birtaniya a makon jiya ne da cewa su ne su ka daure gindin cigaba da wanzuwar haramtaccen gidan rediyon.
Gidan rediyon, wanda mallakar kungiyar fafatukar samun ’yancin kan Biyafara ta MASSOB ce, ya yi kaurin sun a wajen yada kalaman nuna kiyayya ga kasancewar Nijeriya a matsayi kasa daya al’umma daya.
Jagoran fafutukar neman ’yancin, Nnamdi Kanu, mai lasisin zama dan kasar ta Ingila kuma darakta ne a kamfanin, wanda daga bisani ya amshi ragamar gidan rediyon bakidaya. Lai ya yi zargin cewa, Birtaniya ta yi sakacin gaske wajen barin gidan rediyon ya cigaba da gudanar da ayyukansa a kasarta, duk da cewa ya na yada bayanan nuna kiyayya da rashin zaman lafiya da kuma tunzura jama’a ne.
A sanarwar da ofishin jakadancin Ingilar a Nijeriya ya bayar a Abuja karshen makon nan mai dauke da sa hannun jami’in hulda da ’yan jarida na ofishin, Mr. Joe Abuku, a fusace, ya ce, “Birtaniya ba ta da wata masaniya kan ko Nijeriya ta turo da wakilai kan batun Rediyo Biyafara ba.
“Idan da a ce mun samu wani sako kan bukatar hakan, lallai da za mu duba batun gwargwadon irin shaidun da a ka gabato da su bisa la’akari da cewa, ’yancin fadar albarkacin baki ya na da iyaka.”