Daga CRI Hausa
Ranar 18 ga wata, an yi wa firaministan kasar Pakistan Imran Khan, allurar rigakafin cutar COVID-19 wadda kasar Sin take samarwa.
Tuni rigakafin cutar COVID-19 na kasar Sin suka iso wasu kasashe. Ya zuwa yanzu kasashe fiye da 60 a duniya sun ba da iznin yin amfani da rigakafin na kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, ingancin rigakafin kasar Sin da amfaninsa sun kara samun amincewa a duniya. Haka kuma, shugabannin wasu kasashe sun jagoranci karbar rigakafin cutar COVID-19 da kasar Sin take samarwa, a kokarin bayyana kwarin gwiwarsu kan rigakafin kasar Sin.
A kwanakin baya sabon rukunin rigakafin da kamfanin SINOVAC na kasar Sin yake samarwa suka iso birnin Rio de Janeiro, hedkwatar kasar Brazil, wannan ya nuna cewa, an dawo da yi wa mazauna wurin rigakafin daga ranar 17 ga wata, wanda aka dakatar da aikinsa a ranar 12 ga wata. Mazauna wurin suna alla-alla wajen karbar allurar.
Har ila yau a ranar 17 ga wata, asusun Fiocruz na kwalejin nazarin ilmin likitancin halittu na Brazil ya mika alluran rigakafin cutar COVID-19 dubu 500 a rukuni na farko ga ma’aikatar lafiya ta kasar, wadanda yake samarwa ta hanyar amfani da sinadaran maganin kasar Sin. (Tasallah Yuan)