Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya yi kira da gwamnatin da ta fadad kamfen na wayar da kan mutane game da allurar rigakafin cutar korona da za a shigo da su a watan Fabrairu.
Sa’ad ya bayyana cewar yin haka zai taimaka wajen kawar da rudanin da rashin yarda a tsakanin mutane wanda shine yanzu ya kasance abinda ya zama ruwan dare game duniya a Nijeriya.
Sarkin ya bayyana haka n ne a taron wayar da kan malamai da limaman kasar nan game da shi maganin rigakafin Korona da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na kasa NPHCDA ta shirya ranar Laraba.
Sultan ya kara da cewa lallai fa yana kira da gwamnati ta maida hankalinta wajen wayar da kan mutane domin a gujewa shi rudanin da ake yadawa cewa wai maganin an kirkiro shi ne domin a kashe ko kuma rage yawan mutanen nahiyar Afirka.
“Yin allurar rigakafin korona kyauta ne amma amincewa da yin allurar ya rage ga su al’ummar kasa.
Yayin da cutar ke ci gaba da yaduwa a kasashen duniya na kokawar samun maganin rigakafin cutar domin samar wa mutanen su kariya.
Duk da haka kasashen duniya na kokarin wayar da kan mutanen su domin amincewa da ayi allurar rigakafin.
Ministan lafiya Osagie Ehanire ya ce Nijeriya za ta karbi kwalaben maganin rigakafin guda 100,000 a watan Faburairu.
Bayan haka ministan ya kuma ce kamfanin Gabi ya ba Nijeriya gudunmawar kwalaben maganin guda miliyan 42.
Ya ce duk waannan maganin zai isa a yi wa kashi 20 ne rigakafin cutar a kasar nan.
Ehanire ya ce gwamnati ta ware kudade ne domin sayo miliyan 10 na kwalaben maganin rigakafin.