Rigimar Mai Sarrafa Fina-Finai A Amurka Bata Ƙare Ba

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya faɗi jiya Lahadi cewa, ya fara ɗaukar matakin janye lambar girma ta Faransa mai suna “Legion of Honor” da aka taɓa bai wa Weinstein, wadda ita ce karramawa mafi daraja a ƙasar Faransa kuma ɗaya daga cikin lambobin yabo mafiya dajara a duniya.

A shekarar 2012 ce ƙasar Faransa ta bai wa Weinstein wannan lambar yabon, saboda rawar da ya taka wajen yaɗa silima ɗin Faransa da na sauran ƙasashen Turai a duniya.

Wasu ‘yan wasan kwaikwayon Faransa huɗu na daga cikin mata 13 da ke zargin Weinstein da aikata batsa da kuma ƙoƙarin yin lalata da su cikin tsawon shekaru goma da su ka gabata.

Wannan babbar cikas da Weinstein ya samu, ya zo ne kwana guda bayan da Cibiyar Fasaha da Kimiyyar Hotunan Majigi ta Amurka, ta kaɗa ƙuri’ar gaggauta cire Weinstein. A makon jiya ita ma cibiyar Silima din Burtaniya ta dakatar da Weinstein.

Hatta kwamitin gudanarwar kamfanin Weinstein, mai suna Weinstein Co. ya kore shi, bayan wani rahoton jaridar New York Time mai cike da abin fallasa, inda mata wajen 13 ɗin su ke zarginsa da aikata batsa da kuma neman yin lalata da su.

Exit mobile version