Connect with us

WASANNI

Rikici Ya Barke Tsakanin Arsenal Da Bukayo Saka

Published

on

Rikici ya sake barkewa tsakanin shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da dan wasan kungiyar, Bukayo Saka, bayan da dan wasan yaki amincewa da sabon kwantiragin da kungiyar tayi masa tayi.

Matashin dan wasan mai shekara 18 a duniya ya buga wasa mai kyau a wannan kakar ta shekarar 2019 zuwa 2020 duk da cewa a bangaren baya kociyan kungiyar na yanzu yake amfani dashi sai dai dan wasan ya bayyana cewa baya son buga wasa a bangaren baya.

Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ce dai take bibiyar dan wasan bayan wanda matashi ne kuma har yanzu bai sake sabon kwantiragi da Arsenal din ba sai dai banda Dortmund akwai kungiyoyin da suma suke bibiyar halin da ake ciki.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta bayyana cewa tana son dan wasan wanda yake buga wasa a tawagar ‘yan kasa da shekara 19 a Ingila duk da cewa asalinsa dan Nigeriya ne kuma har yanzu yana da damar bugawa tawagar Super Eagles ta Nigeriya wasa.

Sai dai itama kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta tuntubi matashin dan wasan wanda asalinsa yake buga wasa a matsayin dan gaba amma ya koma buga wasa a bangaren baya a kafar hagu tun bayan zuwan Mikel Arteta kungiyar.

Har ila yau Dortmund zata iya sayan dan wasa Saka domin ya maye mata gurbin Jardon Sancho wanda Manchester United take fatan saya fam miliyan 100 a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bana idan an bude.

A kwanakin baya kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana cewa yana son Saka ya ci gaba da zaman kungiyar kuma yana fatan zai shawo kan dan wasan domin ya sake sabuwar yarjejeniya da Arsenal din kafin karshen kakar wasa.

 
Advertisement

labarai